Kungiyar hadakar Yarbawa ta yi taron sirri da Obasanjo kan yadda za su hambarar da Buhari a 2019

Kungiyar hadakar Yarbawa ta yi taron sirri da Obasanjo kan yadda za su hambarar da Buhari a 2019

Yayin da zabukan shekarar 2019 ke dada kara matsowa, tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo a jiya ya ziyarci hadakar kungiyar hadin kan al'ummar Yarbawa ta Afenifere a garin Akure, babban birnin jihar Ondo.

Bangarorin biyu dai kamar yadda muka samu sun tattauna ne a sirrance sai dai majiyar mu ta tabbatar mana da cewa abun da suka tattauna bai rasa nasaba da yadda za su hada karfi da karfe waje daya wajen ganin sun hambarar da gwamnatin shugaba Buhari a 2019.

Kungiyar hadakar Yarbawa ta yi taron sirri da Obasanjo kan yadda za su hambarar da Buhari a 2019

Kungiyar hadakar Yarbawa ta yi taron sirri da Obasanjo kan yadda za su hambarar da Buhari a 2019

KU KARANTA: An daure yan Najeriya 2 a Birtaniya (Dalili)

Legit.ng ta samu cewa a kwanan baya ne dai hadakar fatattakar Buhari a 2019 din ta dargaje a cikin watan jam'iyya mai sunan African Democratic Congress (ADC) domin cimma burin na su.

A wani labarin kuma, Babban malamin addinin kirista kuma shugaban 'yan darikar Katolika mazauna garin Abuja mai suna John Onaiyekan ya sha alwashin jagorantar dubun dubatar jama'a mabiyan sa domin yi wa shugaba Muhammadu Buhari zanga-zanga.

Kamar dai yadda ya shaidawa manema labarai, zanga-zangar da suka shirya yi wa Buhari din na da nasaba da yadda suka ce yayi wa harkar tsaron kasar rikon sakainar kashi a na kashe kiristoci musamman ma a shiyyar Arewa ta tsakiya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel