Karuwai daga Najeriya sun labarta yadda rayuwar su take a kasar Turai

Karuwai daga Najeriya sun labarta yadda rayuwar su take a kasar Turai

Akalla jiga-jigan masu safarar karuwai zuwa kasar turai sha shidda ne suka soma fuskantar shari'a a kasar Faransa a kan yadda suka tilastawa wasu mata daga Najeriya shiga karuwanci.

Sai dai mun kuma samu cewa karuwan da akalla suka kai takwas daga cikin arba'in da tara ne suka soma bayar da ba'asi kan yadda suke rayuwa a gaban kotun tun bayan da aka tilasta masu yin gurbatacciyar sana'ar.

Karuwai daga Najeriya sun labarta yadda rayuwar su take a kasar Turai

Karuwai daga Najeriya sun labarta yadda rayuwar su take a kasar Turai

KU KARANTA: Sanata Alhassan ta sha ruwan duwatsu

Legit.ng ta samu cewa karuwan da suka maida ba'asi, sun bayyana cewa suna shan bakar azaba da ta hada da ta fyade da kuma kin biyan su kudi da kwastomomin su ke yi a wasu lokuta.

A wani labarin kuma, Yayin da zabukan shekarar 2019 ke dada kara matsowa, tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo a jiya ya ziyarci hadakar kungiyar hadin kan al'ummar Yarbawa ta Afenifere a garin Akure, babban birnin jihar Ondo.

Bangarorin biyu dai kamar yadda muka samu sun tattauna ne a sirrance sai dai majiyar mu ta tabbatar mana da cewa abun da suka tattauna bai rasa nasaba da yadda za su hada karfi da karfe waje daya wajen ganin sun hambarar da gwamnatin shugaba Buhari a 2019.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel