Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss zai rantsar da wasu da aka ba mukamai

Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss zai rantsar da wasu da aka ba mukamai

Jiya da rana ne mu ka samu labari daga Jaridar Punch cewa Mai Girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da wasu sababbin nadi a Hukumar da ke kula da kan iyaka na kasar.

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana wannan da kan sa a wajen wani taro da aka shirya domin lura da kan iyakokin kasar. A Ranar Litinin dinnan ne dai aka yi wannan taro na musamman na kwana guda.

Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss zai rantsar da wasu da aka ba mukamai

Sakataren Gwamnati ne zai rantsar da wadanda aka ba mukami

An nada mutane daga kowane bangare 6 na kasar nan wanda za su yi aiki da Hukumar da kuma Gwamnonin Jihohin Kasar da wasu Ministoci da Hafsun Sojoji da sauran Ma’aikatan na Hukumar kula da kan iyakokin Najeriya.

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya sanar da wadanda aka nada wannan aiki cewa su sun fa aikin su shi ne tsare iyakokin kasar nan. Osinbajo ya kuma nemi wadanda aka ba wannan mukamai su tsaya su yi aiki tukuru.

A yau Talata ne za a rantsar da wadannan mutane da aka ba mukami a ofishin na Mataimakin Shugaban kasa. Sakataren Din-din-din a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya Olusegun Adekunle ya bayyana mana wannan.

KU KARANTA:

Mataimakin Shugaban Kasa da kan sa Farfesa Yemi Osinbajo ne zai Shugabanci wannan Hukumar da ke kula da kan iyakar Najeriya. Haka kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ne zai rantsar da wanda aka ba mukaman.

A cikin Hukumar akwai Ministocin Tarayyar kasar nan da su ka hada da Abubakar Malami (SAN); Mansur Dan-Ali; Abdulrahman Dambazzau; Geoffrey Onyeama; Babatunde Fashola (SAN); Udo Udoma; da IG na ‘Yan Sanda da kuma NSA.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel