Tsohon Gwamnan CBN yana nema ayi wa tsarin mulki da Shugabancin kasa garambawul

Tsohon Gwamnan CBN yana nema ayi wa tsarin mulki da Shugabancin kasa garambawul

- Wasu sun fara yin kira a maida wa’adin Shugaban kasa guda tal

- An kuma nemi a rika yin tsarin yi-in-ba-ka a wajen mulkin kasar

- Soludo ya nemi a kuma kirkiro wata sabuwar Jiha a Kasar Kudu

‘Daya daga cikin tsofaffin Gwamnan babban Bankin Najeriya Farfesa Charles Soludo yace zai yi kyau ace an kayyade wa’adin Shugaban kasa zuwa guda kurum a Najeriya har da ma Gwamnonin Jihohi.

Tsohon Gwamnan CBN yana nema ayi wa tsarin mulki da Shugabancin kasa garambawul

Farfesa Soludo yace ana bukatar karin Jiha a Kasar Inyamurai

Farfesa Charles Soludo wanda masani ne kan harkar tattalin arziki ya kuma ce abin da ya dace shi ne a rika juya mulkin kasar nan yadda kowane bangare zai taba. Soludo ya bayyana wannan ne da yake jawabi a Garin Awka a Jihar Anambra.

Wasu dai na ganin ya kamata ayi wa tsarin kasar garambawul inda har Kungiyar Ohanaze Ndigbo ta goyi bayan tsohon Gwamnan na CBN. Farfesa Soludo ya kuma nemi ace ana amfani ne da Mataimakan Shugaban kasa akalla 6 a Najeriya.

KU KARANTA: Inyamuran Najeriya za su goyi bayan Shugaba Buhari

Masanin tattalin yace zai yi kyau ace kowane Yanki sun fitar da Mataimakin Shugaban kasa domin a rika damawa da kowa. Bayan nan kuma Soludo ya nemi a kirkiro sabuwar Jiha a Kudu maso Gabashin kasar tare da kashe kananan Hukumomi.

Ana dai cigaba da kira Shugaba Buhari yayi amfani da matsayar da aka cin ma wajen taron kasar da aka yi a 2014. Daga ciki akwai bukatar a daina amfani da Jihar asalin mutum a rika amfani da Garin da mutum ya zauna na shekara akalla 10.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel