2019: Matasan Najeriya sun nemi Buhari su ci girma su bar wa masu jini a jika

2019: Matasan Najeriya sun nemi Buhari su ci girma su bar wa masu jini a jika

- Matasan Arewa sun nemi Buhari da Atiku su hakura da zaben 2019

- Ana nema Shugaba Muhammadu Buhari ya ba yara masu jini wuri

- Matasan Yankin sun ce ba abin da tsofaffin su ka tsinana a mulki

A jiya mu ka ji cewa wasu tarin Matasan da ke Yankin Arewacin Najeriya sun nemi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar su hakura da takara a 2019.

2019: Matasan Najeriya sun nemi Buhari su ci girma su bar wa masu jini a jika

Wasu Matasa sun ce irin su Atiku Abubakar su ci girma

Bayan wani taro da wasu Matasan Arewa su kayi a Garin Kaduna, an ci ma matsaya cewa manyan ‘yan siyasar yankin da ke shirin takara a zabe mai zuwa watau Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar su hakura da kujerar.

Kakakin tarin Matasan Abdul-Azeez Sulaiman ya bayyana cewa sun yanke shawarar cewa a kyale wani Saurayi mai nagarta da kima irin Buhari ya fito takarar Shugabancin Kasar nan a madadin Dattawan ‘Yan siyasar da ake yi da su har yanzu.

KU KARANTA: Buhari zai yi nasara idan ba mu nan ba – Inji Bukola Saraki

Matasan sun bayyana cewa ana bukatar ‘Dan shekara 18 zuwa 60 ne wajen mulkin Najeriya don haka ya kamata irin su Atiku Abubakar da Shugaba Muhammadu Buhari masu shekaru 70 su hakura su bar wa yara shugabancin Najeriya.

Haka-zalika Matasan su kace babu abin da tsofaffin Shugabannin Kasar su ka tsinanawa Najeriya duk da cewa kusan tun bayan ‘yancin kai su ke mulki. Bayan nan Matasan sun ce ba za su biyewa wani bara-gurbin garambawul da ake shiri ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel