Wani likita ya fada hannun hukuma bayan sayen motar miliyan N28 ta hanyar coge

Wani likita ya fada hannun hukuma bayan sayen motar miliyan N28 ta hanyar coge

Hukumar ‘yan sanda a jihar Legas ta nade wani Likita, Michael Thompson Williams, mai shekaru 28 bayan ya damfari masu sayar da mota miliyan N28m ta hanyar yi masu a-lat din bogi.

Likitan na amfani da wata fasahar zamani ta yanar da sunan kasuwanci domin aika laifuka masu alakar kai tsaye da damfara. Likitan ya yi aiki da wasu fitattun asibitai a garin Legas.

Ana zargin likitan da kutse, ta hanyar gizo, cikin asusun ajiyar mutane na banki da kuma wasu cibiyoyin hada-hadar kudi kuma ta hakan yake iya daukan kudi daga asusun mutane da katin sa na banki.

Wani likita ya fada hannun hukuma bayan sayen motar miliyan N28 ta hanyar coge

Edal Imohim, Kwamishinan 'yan sandan jihar Legas

Likita Williams ya bayyana cewar ya koyi irin wannan shu’umanci a kasar Canada, amma sai daga baya ne, a cewar sa, ya fara amfani da irin wadannan dabaru domin damfarar jama’a.

DUBA WANNAN: Jami'an 'yan sanda sun nade wasu 'yan wala-wala

Sa’a ta karewa Likita William ne a ranar 23 ga watan Maris bayan wani mai garejin sayar da motoci, Adidogun Adewale, ya shigar da korafi ofishin ‘yan sanda kan cewar, Likitan ya sayi motocin alfarma a wurin shi kuma ya biya shi kudin ta hanyar yanar gizo amma da ya je banki sai suka shaida masa cewar babu kudin da ya shiga asusun sa.

Da ake gabatar da Likita Williams ga manema labarai a jiya, Litinin, kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Mista Edgal Imohimi, ya shaidawa manema labarai cewa tuni Williams ya tabbatar masa da aikata laifin yayin hirar su tare da bayyana cewar nan bada dadewa ba zasu gurfanar das hi a gaban kotu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel