Kungiyoyin asiri sun yi arangama da juna, kuma basu ji da dadi ba

Kungiyoyin asiri sun yi arangama da juna, kuma basu ji da dadi ba

- Mutane 9 ne suka rasa rayukansu a Awka, jihar Anambra a ranar lahadi. Sakamakon haduwar kungiyoyin asiri biyu dake adawa da juna

- Ana sake samun karuwar rasa rayuka a Najeriya, na ba gaira babu dalili

- Hukumomi sun tashi haikan don kawo karshen kisan kai

Kungiyoyin asiri sun yi arangama da juna, kuma basu ji da dadi ba

Kungiyoyin asiri sun yi arangama da juna, kuma basu ji da dadi ba

An samu labarin cewa, kungiyoyin asirin guda biyu sunyi barazanar kai ma juna hari a lokacin bikin al'adun da akeyi duk shekara na garin. Wanda aka sani da 'Imo Awka' akan dalilan da suka bar ma kansu sani.

Wata majiya tace kungiyoyin biyu suna fada a Amikwo, Awka, inda suka yi barazana ga juna cewa zasu hadu a ranar karshe na bikin.

"Mutane 4 aka kashe a tsakanin Eke Awka, mutane 3 kuma gurin Nkwelle Awka, sai mutum daya gurin asibitin Regina Caeli a Awka.

Koke koken na iyalan mamatan ya yawaita bayan da suka samu labarin ganin gawarwakin yan'uwansu a cikin garin. " inji majiyar.

DUBA WANNAN: PDP zata iya hadewa da tsofin abokai

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya tabbatar da hakan. Yace sama da tsageru 11 aka kama kuma sun tabbatar da hannun su a kisar a special Anti-robbery Squad da special Anti Cult Unit.

Mohammed yace" Hukumar ta bazama don tsamo wadanda ke da ruwa da tsaki gurin wannan mummunan aikin bayan samu bayanai da mukayi na maboyar su. "

Ya tabbatar da cewa wadanda ke da sa hannu a kisar zasu fuskanci hukunci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel