An kwata: Mamba a majalisar wakilai ya bankado cushe a kasafin kudin bana

An kwata: Mamba a majalisar wakilai ya bankado cushe a kasafin kudin bana

Tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai, Abdulmuminu Jinbrin Kofa, ya bankado wasu zarge-zargen cushe a kasafin kudin bana da majalisun kasa suka zartar das hi satin day a wuce.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewar, Kofa, ya bayyana hakan ne a shafin san a dandalin sada zumunta (Tuwita). Kasa da watanni uku kenan da dawowar Kofa daga dakatarwar da majalisar tayi masa a kan badakalar cushea kasafin kudin bara.

Na dawo majalisa na koma bakin aiki, na dawo a daidai lokacin da kasafin kudin bana ke gaban majalisa. Babu wani canji da aka samu dangane da yadda ake gudanar da al’amuran zartar da kasafin kudi tun shekarar 2016.

An kwata: Mamba a majalisar wakilai ya bankado cushe a kasafin kudin bana

Doga da Kofa ana kus-kus

A cikin satin nan zan bayyanawa jama’a wasu muhimman bayanai a kan kasafin kudin bana da majalisa ta zartar, kuma zan amsa tambayoyin jama’a,” a cewar Kofa.

Tun a ranar Laraba da ta gabata ne Kofa ya fara kwarmata maganar cushe a kasafin kudin bana a lokacin da shugabannin majalisar suka shiga wata ganawa kafin zartar da kassafin kudin.

DUBA WANNAN: An karrama tsohuwar Ministar Buhari a Turai (Hotuna)

Bayan fitowar shugabannin majalisar daga taron, an ga Kofa ya nufi inda shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ke zaune rike da kwafi na kasafin kudin inda suka yi kus-kus.

An dakatar da Kofa ne a watan Satumba na shekarar 2016 bayan barkewar wata badakalar cushe a kasafin kudin kasa. Kofa ya zargi Dogara da wasu shugabannin majalisar wakilai da yin cushen fiye da biliyan N30bn a cikin kasafin kudin shekarar 2016.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel