Dubun wasu Matasa barayi masu fashi da bindigar roba ta cika

Dubun wasu Matasa barayi masu fashi da bindigar roba ta cika

- Masu iya Magana kan ce rana dubu ta barawo daya kuma ta mai kaya

- Asirin wasu ci ma zaune ya tonu yayinda suke shirin aika-aika

Asirin wasu Matasa barayi masu fashi da bindigar roba ya cika kewayen tashar Ketu yayinda suke yunkurin kwacewa wani Mutum motarsa da bindigar roba.

Dubun wasu Matasa barayi masu fashi da bindigar roba ta cika

Dubun wasu Matasa barayi masu fashi da bindigar roba ta cika

Rundunar ‘Yan sanda ta jihar Legas ta yi holar Matasan biyu wadanda ta ce am samu nasarar damke su ne da safiyar yau.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An damke yan fashin bankin Offa da ake nema ruwa a jallo

Fashi da bindigar roba dai na neman zama ruwan dare, inda ko a bayan Legit.ng ta kawo muku yadda wasu Matasa suka bayyana Yadda suke yiwa mutane fashi da bindigar roba

Amma kuma rundunara 'Yan sanda dai na cigaba da samun nasara a kokarinsu na dakile yaduwar aikata laifuka a cin al'umma da kuma bazuwar mallakar makalai ba bisa ka'ida ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel