Tsohuwar ministar Buhari ta samu lambar yabon iya shugabanci ta Duniya (Hotuna)

Tsohuwar ministar Buhari ta samu lambar yabon iya shugabanci ta Duniya (Hotuna)

Wata jaridar nahiyar Turai (Fortune Magazine) ta karrama tsohuwar minista a Najeriya kuma mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina J. Mohammed.

Jaridar ta karrama Amina ne saboda kokarin ta a kan inganta muhalli da kuma iya salon shugabanci. Jaridar ta bawa Amina lambar yabo ta "gwarzuwar kare muhalli" tare da saka ta cikin jerin shugabannin duniya.

Kafin zabar ta a matsayin mataimakiyar sakataren Majalisan Dinkin Duniya (MDD), Amina, ta kasance ministar muhalli a Najeriya karkashin gwamnatin shugaba Buhari.

Tsohuwar ministar Buhari ta samu lambar yabon iya shugabanci ta Duniya (Hotuna)

Tsohuwar ministar Buhari ta samu lambar yabon iya shugabanci ta Duniya

A wani labari da Legit.ng ta wallafa a jiya kun ji cewar, shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) na rikon kwarya, Ibrahim Magu, ya zama shugaban gamayyar hukumomin yaki da cin hanci na kasashen kungiyar Commonwealth dake nahiyar Afrika.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa na kulle-kullen hallaka ni - Gwamna Wike

Shugabannin hukumomin sun amince da zaben Magu a matsayin shugaba a karshen wani taro na kwanaki biyar da suka kamma a birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Taron na shugabannin hukumomin yaki da cin hanci ya tattauana a kan yadda za a shawo kan matsalolin wawure dukiyar kasashen Afrika da wasu shugabanni ke yi tare da jibge su a kasashen ketare tare da tattauna hanyoyin da za a bi domin kwato wadanda aka karkatar a ciki da wajen nahiyar Afrika.

Tsohuwar ministar Buhari ta samu lambar yabon iya shugabanci ta Duniya (Hotuna)

Tsohuwar ministar Buhari ta samu lambar yabon iya shugabanci ta Duniya

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel