Fadar Shugaban kasa ta gargadi ‘yan Najeriya game da kada shugaba Buhari a zaben 2019

Fadar Shugaban kasa ta gargadi ‘yan Najeriya game da kada shugaba Buhari a zaben 2019

- Fadar shugaban kasa tayi gargadin cewa idan shugaba Buhari ya fadi zabe mulki ya koma hannun jam’iyyar PDP zasu rusa duk wani kokari da tsari da wannan gwamnatin ta kawo tun lokacin hawanta mulki a 2015

- Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana cewa ‘yan jam’iyyar PDP suna zagaya kasa suna cewa “a canja canji” domin kawar da gwamnatin APC daga kan mulki

- Duk da cewa gwamnatin PDP sune suka kafa jami'ar yaki da rashawa a Najeriya, amma a yanzu kawar da shugaba Buhari daga bisa mulki zai mayar da kasar zuwa ‘yar gidan jiya na cigaba da aikata rashawa

Fadar shugaban kasa tayi gargadin cewa idan shugaba Buhari ya fadi zabe mulki ya koma hannun jam’iyyar PDP zasu rusa duk wani kokari da tsari da wannan gwamnatin ta kawo tun lokacin hawanta mulki a 2015.

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana cewa ‘yan jam’iyyar PDP suna zagaya kasa suna cewa “a canja canji” domin kawar da gwamnatin APC daga kan mulki.

Duk da cewa gwamnatin PDP sune suka kafa jami’ar yaki da rashawa a Najeriya, amma a yanzu kawar da shugaba Buhari daga bisa mulki zai mayar da kasar zuwa ‘yar gidan jiya na cigaba da aikata rashawa, sannan kuma kudaden da aka karba daga hannun barayin gwamnati zasu koma hannun wadanda aka karba daga wurinsu.

Fadar Shugaban kasa ta gargadi ‘yan Najeriya game da kada shugaba Buhari a zaben 2019

Fadar Shugaban kasa ta gargadi ‘yan Najeriya game da kada shugaba Buhari a zaben 2019

KU KARANTA KUMA: Kalli ma’uratan da Allah ya baiwa kyautar yan shida bayan shekaru 17 da aure ba tare da haihuwa ba

Sannan kuma Ofishin ya kara bayyana cewa wannan gwamnatin ta kirkiro abubuwa da dama na cigaba wadanda idan har aka cire shugaba Buhari daga bisa mulki zai lalata al’amuran musamman na bayar da bayani game da dukiyar da ka mallaka (VAIDS) da kuma tona asirin barayin gwamnati.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel