Dino Melaye ya taya sababbin Shugabannin APC na Jihohi murna

Dino Melaye ya taya sababbin Shugabannin APC na Jihohi murna

- Fitaccen ‘Dan Majalisar APC ya caccaki Jam’iyyar mai mulki

- Sanata Dino Melaye yayi magana kan rikicin da ya barke a APC

- Kusan Jihohi da dama an samu ‘Yan ta-ware a Jam’iyyar APC

‘Daya daga cikin manyan ‘Yan Majalisar Jam’iyyar a Najeriya ya caccaki Jam’iyyar mai mulki a game da zaben da aka gudanar da shugabannin Jam’iyyar a Jihohi da kuma Kananan Hukumomi.

Dino Melaye ya taya sababbin Shugabannin APC na Jihohi murna

Sanata Dino Melaye ya sa baki kan rikicin cikin gida na APC

Sanatan na APC yayi amfani da shafin sa na sada zumunta inda ya taya sababbin Shugabannin da aka nada murna. Dino Melaye dai yace yana taya shugabannin APC na Jihohi har 72 da aka samu farin cikin wannan matsayi.

KU KARANTA: Yaron El-Rufai da Jikar Isiyaka Rabi'u sun yi fada a bainar Jama'a

‘Dan Majalisar na APC Dino Melaye dai yayi wa Jam’iyyar sa gatse ne a kaikaice saboda rikicin da ake yi a Jam’iyyar a Jihohi fiye da 20. Sanatan na Yammacin Jihar Kogi ya kara da cewa lallai Jam’iyyar ta dace da samun rabuwar kai.

Yanzu haka dai an samu shugabannin dabam-dabam a Jihohi irin su Legas, Kaduna, Abia, Oyo, Bayelsa da kuma Kwara an samu bangorori inda kowa yake ikirarin shi ne Shugaban Jam’iyyar na Jiha. Har yanzu dai an kasa shawo kan rigimar.

Dama kun ji cewa a Jihar Kogi inda Sanatan ya fito ana ta faman rikici tsakanin tsofaffin Shugabannin Jam’iyyar da aka kora da bangaren Gwamna Yahaya Bello wanda duk ba su jituwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel