Kungiyar APC Aqida na barazanar barin jam'iyyar APC

Kungiyar APC Aqida na barazanar barin jam'iyyar APC

Wata kungiya mai suna APC Aqida, wacce wasu 'yan takarar gwamna a jihar Katsina suka kafa, sun yi barazanar barin jam'iyyar APC mai mulki, saboda irin matsalolin da jam'iyyar take fama dashi na rashin dai-dai to

Kungiyar APC Aqida na barazanar barin jam'iyyar APC

Kungiyar APC Aqida na barazanar barin jam'iyyar APC

Wata kungiya mai suna APC Aqida, wacce wasu 'yan takarar gwamna a jihar Katsina suka kafa, sun yi barazanar barin jam'iyyar APC mai mulki, saboda irin matsalolin da jam'iyyar take fama dashi na rashin dai-dai to. A wata sanarwa da shugaban kungiyar, Sanata Mohammed Liman, da sauran shugabannin kungiyar irin su, Dokta Usman Bugaje, Alhaji Sada Ilu da Sanata Sadiq Yar'adua, sun bayyana babban taron jam'iyyar nan a matsayin abin kunya ga jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Yanzu - Yanzu: 'Yan Sabuwar jam'iyyar nPDP sun kai ziyara APC hedkwatar

Sun bayyana cewar sunyi ta jira don ganin cewa jam'iyyar ta dawo yanda take, sannan kuma ta kawo tsari mai amfani ga 'yan jam'iyyar amma har yanzu ba wani cigaba da aka samu. Kungiyar tace, "Babban taron jam'iyyar APC babban abin kunya ne ga jam'iyyar da ma kasa baki daya.

Kungiyar tace a jihar Katsina wanda ita ce mazabar shugaban kasar Najeriya, har yanzu ba'a sayar da form din takara ba ga da yawa daga cikin masu son fitowa takara jihar. Sai dai sunce hakan ba wai abin mamaki bane ganin yanda jam'iyyar take so ta karfi sai ta karawa kanta lokaci.

Wannan shine dalilin da yasa muka kafa kungiyar APC Aqida a cikin jam'iyyar APC don kawo cigaba da dai-dai to ga jam'iyyar.

"Saboda haka a matsayin mu na 'yan kasa na gari, muna da 'yancin da zamu iya canja jam'iyya tunda wannan da muke ciki bata san darajar mutunta mambobinta ba, sannan kuma jam'iyyar bata da wani tsari na kawo cigaba ga 'ya'yanta, don haka a shirye muke mu canja sheka a kowanne lokaci," inji kungiyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel