Karya ne, Magu baya neman zama Gwamnan Borno - EFCC

Karya ne, Magu baya neman zama Gwamnan Borno - EFCC

- EFCC ta barranta shugabanta da rahoton tsayawar shugabanta takarar kujerar Gwamna

- Wata Jarida a kafar sadarwa ta zamani ce dai ta wallafa rahoto shirin takarar Magun

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta karyata wani rahoto da ya bulla a yanar gizo da yake cewa wai shugaban hukumar yana shirye-shiryen neman zama Gwamnan jihar Borno.

A kawo mana dauki, Watanmu 44 ba a biya mu albashi ba – Ma’aikata

A kawo mana dauki, Watanmu 44 ba a biya mu albashi ba – Ma’aikata

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani martini da ta fitar dake nuna rashin jin dadin rahoton da wata jaridar ta kafar sadarwa a yanar gizo ta wallafa a shafinta mai suna 247ureports.com, inda EFCC ta ce shugabanta ba dan siyasa ba ne kuma baya neman wata takara.

KU KARANTA: Shekarau da Wali zasu bayyana Ofishin EFCC a yau, akan maganar kudin kamfen N950m

247ureports.com dai ta wallafa a shafinta cewa, “Ganawar da shugaba Buhari yayi da Ali Madu Shariff wani yunkuri ne na fara shirye-shiryen kaddamar da takarar Magu”

A kawo mana dauki, Watanmu 44 ba a biya mu albashi ba – Ma’aikata

A kawo mana dauki, Watanmu 44 ba a biya mu albashi ba – Ma’aikata

A sakamakon haka ma hukumar ta ce tana duba yiwuwar shigar da Jaridar da ma sauran wadanda suka wallafa rahoton kara domin rahoton tamkar wani yunkuri ne na batawa mukaddashin hukumar suna. Kuma yunkurin hada shugaban da takarar siyasa hakika cin zarafi ne kololuwa.

A cikin satin da ya gabata ne dai aka zabi Ibrahim Magu shugaban kungiyar shuwagabannin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa ta kasashen Africa rainon Ingila.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel