Gwamnatin tarayya na kulle-kullen hallaka ni – Wani gwamnan PDP

Gwamnatin tarayya na kulle-kullen hallaka ni – Wani gwamnan PDP

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, y ace gwamnatin tarayya na shirin kasha shi a cikin taron jama’a tare da dora alhakin mutuwar sa a kan hatsari.

Wike na wadannan kalamai ne a jiya, Lahadi, yayin gudanar da addu’o’in cikar sa shekaru 3 a kan karagar mulki a wata Cocin Living Faith dake D – Line a Fatakwal.

Gwamnan ya ce,” bayanan sirri da na samu da safiyar yau ya nuna cewar ana kulle-kullen kashe ni a wurin taro tare da dora alhakin mutuwa ta a kan hatsari.”

Wike ya kara da cewar yunkurin gwamnatin tarayya na kasha shi ba zai girgiza shi ko yi masa barazana a kokarin san a kare jihar Ribas da kuma dimokradiyya ba.

Gwamnatin tarayya na kulle-kullen hallaka ni – Wani gwamnan PDP

Nyesom Wike

Sannan ya kara da cewa duk wani mugun nufi ba zai tasiri a kan sa ba saboda Allah zai cigaba da kare shi ko don gaskiya, da ya ce, ya rike.

Gwamnan ya bayyana cewar gwamnatin APC tayi yunkurin yin amfani da hukumar ‘yan sanda domin boye miyagun makamai da makudan kudi a gidan san a Abuja domin kawai su samu uzurin ci masa mutunci, amma sai kotu ta hana su binciken gidan na sa bayan sun je sun boye makaman a gidan.

DUBA WANNAN: Babban burina a Duniya – Aliko Dangote

Gwamnan bai ambaci sunan wani mutum ko kungiya dake kokarin kasha ba, sannan bai fadi dalilin da yasa wasu ko gwamnatin tarayya ke kokarin kasha shi ba.

Babban darektan hukumar kula da iyakokin ruwa na kasa kuma dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a zaben 2015, Dakuku Peterside, y ace mutanen jihar Ribas zasu yiwa gwamna Wike ritaya daga siyasa a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel