Mutane na rububin sayen bindigogina daga ko ina a fadin Najeriya - Mai laifi

Mutane na rububin sayen bindigogina daga ko ina a fadin Najeriya - Mai laifi

- Hukumar ‘yan Sandan Niger tayi nasarar kama wasu mutane hudu masu hada bindigogi a Zungeru dake karamar hukumar Wushishi

- Mutanen da ake zargin sune Badamasi Umar mai shekaru 54, Adamu Aliyu mai shekaru 45, Kabiru Tukura mai shekaru 40, sai kuma Isyaku Madaki mai shekaru 40

- Muhammadu Abubakar mai magana da yawun kungiyar kato da gora, yace wadanda aka kaman sun amsa laifinsu sannan kuma an samu bindigogi kirar baushe 12 a hannunsu

Hukumar ‘yan Sandan Niger tayi nasarar kama wasu mutane hudu masu hada bindigogi a Zungeru dake karamar hukumar Wushishi.

Mutanen da ake zargin sune Badamasi Umar mai shekaru 54, Adamu Aliyu mai shekaru 45, Kabiru Tukura mai shekaru 40, sai kuma Isyaku Madaki mai shekaru 40.

Umar ya bayyana cewa ya dade cikin harkar kasuwancin bindigogin, sakamakon haka ma mutane da dama daga wurare na fadin kasar na suke zuwa sayen bindigoginsa. Umar yace cikin wadanda ke sayen bindigogin nasa sun hada hadda kamfaninnikan tsaro da kuma kungiyoyin kato da gora.

Mutane na rububin sayen bindigogina daga ko ina a fadin Najeriya - Inji wanda aka kama

Mutane na rububin sayen bindigogina daga ko ina a fadin Najeriya - Inji wanda aka kama

Umar ya kara da cewa bai san cewa an hana kasuwancin makamai ba tare da izinin dokar kasa ba, yace da ya san da wannan labari da tuni ya daina wannan sana’ar.

KU KARANTA KUMA: Manyan jiga-jigan PDP sun ziyarci Sanata Jang a gidan yari

Muhammadu Abubakar mai magana da yawun kungiyar kato da gora, yace wadanda aka kaman sun amsa laifinsu sannan kuma an samu bindigogi kirar baushe 12 a hannunsu

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel