Akwai kishin-kishin din za a kuma dakatar da Sanata Ndume da Omo-Agege

Akwai kishin-kishin din za a kuma dakatar da Sanata Ndume da Omo-Agege

- Ana binciken wasu Sanatocin Jam’iyyar APC a Majalisar Dattawa yanzu

- Majalisar na ganin da hannun Agege da Ndume wajen dauke Sandar girma

- Ana dai iya kuma dakatar da Sanatocin idan har kwamiti ta same su da laifi

Bisa dukkan alamu dai Sanatocin Jam’iyyar APC kuma wadanda ake tunani su na tare da Shugaban kasa Buhari watau Ovie Omo-Agege da Ali Ndume za su gamu da matsala babba a makon nan. Kwanan nan aka dakatar da Omo-Agege.

Akwai kishin-kishin din za a kuma dakatar da Sanata Ndume da Omo-Agege

Watakila a kuma dakatar da Sanata Ndume daga Majalisa

Mun samu labari cewa ba mamaki a makon nan Majalisar Dattawa ta kara dakatar da Sanata Ali Ndume da kuma Ovie Omo-Agege. Kwanakin baya aka zargi Sanata Omo Agege da amfani da tsageru wajen dauke sandar Majalisar.

Wani kwamti da Sanata Bala Ibn Na’Allah ya jagoranta sun yi bincike game da kusten da aka yi wa Majalisar kwanaki inda su ka mika rahoton su ga Sanata Samuel Anyawu wanda zai yankewa Sanatocin na Jam'iyyar APC hukunci.

KU KARANTA: Wane mutum: Buhari ba zai kai labari ba idan ba mu nan – Saraki

A binciken da Majalisar ta gudanar, wani babban Jami’in tsaro Abdul Sulu-Gambari ya bayyana cewa Sanata Ali Ndume ne ya hana Jami’an ‘Yan Sanda karbe sandar girman Majalisar lokacin da tsageru su ka shigo su kayi ta’adi kwanaki.

Shi dai Sanata Omo Agege ya bayyanawa ‘Yan Sanda cewa babu hannun sa a wajen awon gaba da sandar Majalisar. Binciken da Majalisa tayi dai na nuna cewa an samu Sanatocin da laifi tsamo-tsamo wajen aikata ta’addanci a baya.

Ba mamaki wannan karo ma a dakatar da ‘Yan Majalisar idan har kwamiti ta same su da laifi. A baya dai an dakatar da Sanata Omo Agege saboda nuna goyon bayan sa ga Shugaba Buhari an kuma taba dakatar da Ndume na kwanaki kusan 90.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel