Za a gabatar da taron APC da nPDP yau - Baraje

Za a gabatar da taron APC da nPDP yau - Baraje

A jiya ne wani ginshiki na jam'iyya APC mai mulki a jihar Kwara, kuma shugaban 'yan kungiyar nPDP, Alhaji Kawu Baraje, ya musanta cewar kungiyar nPDP tura sakon dokoki zuwa ga shugabannin jam'iyyar APC a wata wasika da aka aika kwanan nan

Za a gabatar da taron APC da nPDP yau - Baraje

Za a gabatar da taron APC da nPDP yau - Baraje

A jiya ne wani ginshiki na jam'iyya APC mai mulki a jihar Kwara, kuma shugaban 'yan kungiyar nPDP, Alhaji Kawu Baraje, ya musanta cewar kungiyar nPDP tura sakon dokoki zuwa ga shugabannin jam'iyyar APC a wata wasika da aka aika kwanan nan. Baraje wanda yayi magana da manema labarai a Ilorin babban birnin jihar Kwara, ya ce a yau za'a gabatar da taro tsakanin su da shugabannin jam'iyyar APC, sannan kuma zasu nuna musu laifukan su.

Yayin da yake nuna damuwar sa akan irin rikice-rikicen da jam'iyyar mai mulki take fuskanta , yace sakon da nPDP ta tura tayi ne domin kawo karshen wadannan matsaloli da ake fuskanta. Baraje wanda yace jam'iyyar adawa ta PDP bata fuskantar irin wannan matsalolin, yayi gargadin cewar idan jam'iyyar bata yi tunani akan akan bukatar nPDP ba, to a babban taron jam'iyyar da za'a gabatar nan gaba zai zamo taron da za'a bayyana matsayin kowanne bangare.

DUBA WANNAN: El-Rufa'i ne matsalar APC – Jigon Kwankwasiyya

Yayi magana game da murabus din sakataren kungiyar, Prince Olagunsoye Oyinlola, a matsayin alama ta barazar da jam'iyyar take fuskanta mutukar shugabannin jam'iyyar baza su iya saka mabiyansu tsayawa a jam'iyyar ba.

Ya ce 'yan kungiyar nPDP din zasu fara ganawa da sirri da manyan 'yan kungiyar a fadin kasar nan, don dakatar da barazana ga jam'iyyar domin kuwa suna iya barin jam'iyyar ta APC a kowanne lokaci.

Ya ce, "A taro na karshe da aka gabatar a shekarar 2016, na gaya muku cewa hanyar da jam'iyyar take kai ba mai bullewa bace, idan kuka yi duba ga wasikar da muka rubuta, bamu bawa jam'iyyar dokokin da aka ce mun bada ba, amma mun shawarci jam'iyyar akan hanya mai bullewa, sannan kuma mun nuna fushin mu ga jam'iyyar.

"Yanzu jam'iyyar ta gayyace, kwana bakwai bayan rubuta wasikar tamu, inda suka nuna cewar suna so mu hadu, amma saboda muna magana da shugabannin kungiyar da dama a fadin kasar nan, mun nuna musu cewar bazai yiwu mu hadu a rana daya ba. Yanzu sun shirya taron a yau Litinin dinnan da misalin karfe 2 na rana."

Baraje ya sallami magoya bayan kungiyar wanda Sanata Abdullahi Adamu ya jagoranta, inda yace kungiyar nPDP babban ginshiki ce da baza a iya yada ita ba.

"Mun yi tafiya mai nisa tare da jam'iyyar APC, sai a yanzu muke fuskantar irin wadannan matsalolin a jam'iyyar fiye da wanda jam'iyyar PDP ke fuskanta. Idan har shugabannin jam'iyyar sun amsa sunan su, to su nemi hanyar dakatar da matsalolin," inji shi.

Baraje yace, kungiyar tayi na'am da fitowa takarar da shugaban kasa yayi a karo na biyu, inda yace shine ma dalilin da yasa kungiyar ta rubuta wannan takarda zuwa ga shugabannin jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel