Manyan jiga-jigan PDP sun ziyarci Sanata Jang a gidan yari

Manyan jiga-jigan PDP sun ziyarci Sanata Jang a gidan yari

- Wasu daga cikin manya manyan ‘yan siyasar Najeriya a ranar Lahadi sun kai ziyara ga Sanata mai wakiltar Filato ta arewa Jonah Jang, a gidan yari

- Sun kai masa ziyarar ne bayan kwanaki biyar da justice Daniel Longji na kotun jihar Filato dake garin Jos ya bayar da umurnin tsare shi a gidan yari bisa ga zargin dibar kudaden gwamnati ba bisa ka’ida ba

- Jang tare da wani tsohon mai ajiyar kudi na ofishin sakataren gwamnatin jihar ta Filato, Yusuf Pam, aka bayar da umurnin tsaresu a gidan yari har zuwa ranar 24 ga watan Mayu

Wasu daga cikin manya manyan ‘yan siyasar Najeriya a ranar Lahadi sun kai ziyara ga Sanata mai wakiltar Filato ta arewa Jonah Jang, a gidan yari.

Sun kai masa ziyarar ne bayan kwanaki biyar da justice Daniel Longji na kotun jihar Filato dake garin Jos ya bayar da umurnin tsare shi a gidan yari bisa ga zargin dibar kudaden gwamnati ba bisa ka’ida ba.

Jaridar The Punch ta bayar da rahoton cewa, Jang tare da wani tsohon mai ajiyar kudi na ofishin sakataren gwamnatin jihar ta Filato, Yusuf Pam, aka bayar da umurnin tsaresu a gidan yari har zuwa ranar 24 ga watan Mayu, da za’a yanke masu hukunci ko kuma a bayar dasu beli.

Manyan jiga-jigan PDP sun ziyarci Sanata Jang a gidan yari

Manyan jiga-jigan PDP sun ziyarci Sanata Jang a gidan yari

Dukansu biyun an zargesu ne da aikata laifuka 12 a gaban kotun da hukumar yaki da rashawa ta gabatarwa kararsu.

KU KARANTA KUMA: El-Rufa'i ne matsalar APC – Jigon Kwankwasiyya

Zargin duka da suke masu yana da alaka ne da kudaden gwamnatin jihar ta Filato wadanda babban bankin Najeriya ya sakarwa jihar domin gudanar da wasu muhimman ayyuka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel