Buhari zai karbi takardun kasafin kudin 2018 cikin wannan satin - majalisar wakilai

Buhari zai karbi takardun kasafin kudin 2018 cikin wannan satin - majalisar wakilai

- Majalisar wakilai ta bayyana cewa takardun kasafin kasafin kudin Najeriya na 2018, zai kasance a bisa teburin shugaba Muhammadu Buhari cikin sati daya bayan kaddamar da kasafin

- Majlisar Dattawa ta kaddamar da kasafin kun najeriya na 2018 na N9.12trn a ranar Larabar satin da ya gabata bayan gabatar masu dashi da watanni shida

- Ciyaman na kwamitin majalissa a bangaren sadarwa da kuma harkokin jama’a Abdulrazak Namdas, ya bayyana a ranar Lahadi, a birnin tarayya cewa zuwa ranar Laraba ta wannan satin za’a turawa shugaban kasa kasafin kudin

Majalisar wakilai ta bayyana cewa takardun kasafin kasafin kudin Najeriya na 2018, zai kasance a bisa teburin shugaba Muhammadu Buhari cikin sati daya bayan kaddamar da kasafin.

Majlisar Dattawa ta kaddamar da kasafin kun najeriya na 2018 na N9.12trn a ranar Larabar satin da ya gabata bayan gabatar masu dashi da watanni shida.

Buhari zai karbi takardun kasafin kudin 2018 cikin wannan satin - majalisar wakilai

Buhari zai karbi takardun kasafin kudin 2018 cikin wannan satin - majalisar wakilai

Ciyaman na kwamitin majalissa a bangaren sadarwa da kuma harkokin jama’a Abdulrazak Namdas, ya bayyanawa manema labarai na gidan gwamnati, cewa zuwa ranar Laraba na wannan satin za’a turawa shugaban kasa kasafin kudin.

KU KARANTA KUMA: Ma’aikaci ya cizgewa wani dan kasar Indiya hakora 7 saboda bai biya shi albashi ba a Minna

Mataimakin ciyaman na kwamitin majalisar masu tantance doka, Mr. Chris Azubuogu, ya bayyana cewa majalisun biyu na kasa zasu hadu su tattauna a yau (Litinin). Bayan nan zasu bayar da rahotanninsu game da kaddamar da kasafin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel