El-Rufa'i ne matsalar APC – Jigon Kwankwasiyya

El-Rufa'i ne matsalar APC – Jigon Kwankwasiyya

A daidai lokacin da guguwar siyasa ke tasowa, an samu rabuwar kai a jam’iyya mai mulki wato APC, bayan wasu daga cikin tsoffin yan PDP da suka sauya sheka zuwa APC a 2015 suna ganin an maida su saniyar ware.

Sannan kuma sukayi barazanar barin jam’iyyar idan har ba’a dauki mataki akan lamarin ba.

Wannan yasa gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai yace koda sun bar jam’iyyar babu abunda zai hana Buhari cin zabe a 2019.

El-Rufa'i ne matsalar APC – Jigon Kwankwasiyya

El-Rufa'i ne matsalar APC – Jigon Kwankwasiyya

Hakan ya sa wani jigo na' yan sabuwar PDPn, wanda kuma jigo ne a Kwankwasiyya a Jihar Kano, Hon Danburam Nuhu, ya ce maganar da ake yi cewa ko da su, ko ba su za a ci zabe a 2019, ba abu ne da ya dame su ba, saboda ba yau aka fara ba.

Ya kara da cewar matukar ba a tsaya an duba matsalolin da ke cikin jam'iyyar APC ba, to akwai matsala.

Sanann kuma ya ce El-Rufa'i, na daga cikin matsalolin jam'iyyar APC.

KU KARANTA KUMA: Ma’aikaci ya cizgewa wani dan kasar Indiya hakora 7 saboda bai biya shi albashi ba a Minna

Daga karshe ya jadadda cewa babu wani dan siyasar da ya san siyasa da zai fito ya ce 'duk wanda ba zai bi yadda suke so ba ya kama gabansa, cewa ai ba a dole a siyasa.

A halin da ake ciki, ‘daya daga cikin manyan ‘Yan APC a Jihar Kwara kuma Jagoran nPDP Alhaji Kawu Baraje ya bayyana cewa dama can ba su ba Shugaba Buhari wani wa’adi a wasikar da su ka aika masa kwanaki ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan ka samu sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel