2019: Bukola Saraki yace idan babu ‘Yan N-PDP Buhari ba zai yi nasara ba

2019: Bukola Saraki yace idan babu ‘Yan N-PDP Buhari ba zai yi nasara ba

- Shugaban Majalisa Saraki yace sai an yi da su ne APC za ta kai labari

- Tsohon Gwamnan yace babu yadda za ayi Buhari ya ci Kwara sai da su

- Gwamnan Kaduna dai yace ko ‘Yan N-PDP sun ki sai Buhari yaci zabe

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa Shugaba Buhari na bukatar tsofaffin ‘Yan Jam’iyyar PDP da su ka narke cikin tafiyar APC domin ya lashe zabe mai zuwa na 2019.

2019: Bukola Saraki yace idan babu ‘Yan N-PDP Buhari ba zai yi nasara ba

Shugaba Buhari ba zai kai labari ba a 2019 sai yayi da mu inji Saraki

Bukola Saraki ya maida martani ga kalaman wasu manyan ‘Yan APC irin su Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai wanda yace ko babu ‘Yan N-PDP Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai lashe zaben 2019 hankali kwance.

KU KARANTA: Timi Frank yace gara mulkin Jonathan da Shugaba Buhari

Shugaban Majalisar Kasar Bukola Saraki yayi dariya da ya ji wannan maganar inda yace karyar su ta sha karya. Saraki yayi wannan magana ne lokacin da yake Jihar Kwara domin halartar zaben Shugabannin Jam’iyyar Jihar.

Bukola Saraki ya fadawa manyan ‘Yan Jam’iyyar APC na Jihar cewa duk masu ra’ayin cewa Shugaba Buhari ba ya bukatar goyon bayan su domin kawo Jihar Kwara yana yaudarar kan sa ne inda ya kyalkyace da dariyar keta.

Kwanaki ne ‘Yan N-PDP wanda su kayi wa tsohon Shugaban Kasa Jonathan baram-baram su ka aikawa Shugaba Buhari wasika cewa ana yi babu su a Gwamnati. Gwamnan Kaduna El-Rufai yace ko babu su kuwa Buhari ya ci zabe ya gama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel