Tirka tirkar IG Ibrahim da Saraki: Har yanzu wakilan majalisa basu yi ido hudu da Buhari ba

Tirka tirkar IG Ibrahim da Saraki: Har yanzu wakilan majalisa basu yi ido hudu da Buhari ba

Har zuwa ranar Litinin, 21 ga watan Mayu, kwamitin sulhu da shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya kafa da nufin ganawa da shugaban kasa kan bahallatsarsa da sufetan Yansandan Najeriya, basu samu damar ganawa da shugaba Buhari ba.

Daily Trust ta ruwaito a ranar Larabar da ta gabata ne Saraki ya nada kwamitin dake kunshe da Sanatoci 10 da nufin su tattauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan labarin da ya samu na cewa Sufetan na shirin daura masa wasu manyan laifuka.

KU KARANTA: Karamar magana ta zama babba: An hallaka wani Musulmi saboda ya yanka Saniya

Saraki ya bayyana ma majalisar cewa ya fahimci wata tuggu da babban sufetan Yansandan Najeriya ke shirya masa dangane da wasu matasa yan kungiyar matsafa da yansanda suka kama, wadanda suka ce su yaran Saraki ne da gwamnan jihar Kwara.

Tirka tirkar IG Ibrahim da Saraki: Har yanzu wakilan majalisa basu iyo hudu da Buhari ba

Tirka tirkar IG Ibrahim da Saraki

Da wannan ne ya sanya Sanata Saraki ya nada sanatoci goma da suka hada da: Ahmad Lawan, Godswil Akpabio, Olusola Adeyeye, Danjua Goje, Abdullahi Adamu, Sam Egwu, Aliyu Wammako, Fatima Raji Rasak da uwargida jigon APC, Ahmed Bola Tinubu, Oluremi Tinubu, da nufin su gana da Buhari, kuma su kai masa rahoto a ranar Laraba 23 ga watan Mayu.

Sai dai wata majiya ta bayyana cewa har yanzu ba’a baiwa Sanatocin damar ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, inda suke ce ba ayi musu iso ba, don haka basu da hurumin shiga fadar shugaban kasa.

Sai dai wani daga cikin Sanatocin da aka nada ya bayyana ma majiyar NAIJ.om cewa ba shi da tabbacin ko ofishin shugaban majalisar dattawa ta aika ma fadar shugaban kasa takardar neman damar ganin shugaban kasa ba, inda yace shugaban ne ya kamata ya sanar da fadar shugaban kasa zuwansu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel