Idan PDP ta dawo mulki aikin da mu kayi zai dawo danye - Shugaba Buhari

Idan PDP ta dawo mulki aikin da mu kayi zai dawo danye - Shugaba Buhari

- Buhari ya bayyana abin da zai faru idan PDP ta doke shi a zaben 2019

- Mai magana da bakin Buhari yace dai PDP na nema a koma gidan jiya

- Garba Shehu yace Patience Jonathan za ta fi kowa murna PDP ta dawo

Mun samu labari Mai magana da bakin Shugaban Kasa Buhari watau Garba Shehu yayi magana kan irin satar da ake zargin PDP da Iyalin tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan sun tafka a mulki.

Idan PDP ta dawo mulki aikin da mu kayi zai dawo danye - Shugaba Buhari

Garba Shehu yace kul jama'a su kayi gigin cire Shugaba Buhari

Garba Shehu a wata takarda da ya rubuta yake cewa ya kamata ‘Yan Najeriya sun fahimci cewa idan har Shugaba Buhari ya bar kujerar Shugaban kasa bayan 2015 akwai babbar matsala domin kuwa Najeriya za ta dawo gidan jiya.

KU KARANTA: Sakataren yada labaran APC ya soki Buhari ya yabawa Jonathan

Hadimin na Shugaba Buhari yace yaki da barnar da Gwamnatin nan tayi sai dawo danye idan PDP ta karbi mulki. Garba Shehu yace babu wanda zai kai matar tsohon Shugaba watau Patience Jonathan murna idan Buhari ya sha kashi.

Shehu ya caccaki Patience Jonathan inda yace idan PDP ta dawo mulki ba za ta bukaci Lauya domin karbe dukiyoyin da ta Gwamnatin Buhari ta karbe ba. Shehu yace yaki da cin hanci shi ne babban abin da ya kawo Gwamnatin Buhari.

Wani babba a da Jam’iyyar APC mai mulki dai yayi tir da Gwamnatin Buhari inda har ta kai yana ba tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan hakurin cire shi daga mulki da APC tayi a 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel