Mutane 12 sun gamu da ajalinsu a wani hari da yan ta’addan Mali suka kai wata Kasuwa

Mutane 12 sun gamu da ajalinsu a wani hari da yan ta’addan Mali suka kai wata Kasuwa

Akalla mutane goma sha biyu ne suka gamu da ajalinsu a wani hari da yan ta’adda masu rajin Islama suka kai a wata kasuwa dake Arewacin kasar Mali, kamar yadd gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan ta’addan sun kai wannan hari ne a ranar Asabar, 19 ga watan Mayu, a wani gari mai suna Boulekessi dake gab da iyakar kasar Mali da Burkinafaso.

KU KARANTA: Ba duka aka zama daya ba: Kalli yadda wani Dansanda ke gabatar da Tafsirin Al-Qur’ani

Wata majiya daga rundunar Sojin kasar ta bayyana cewa yan ta’addan sun je farautar Sojojin Mali ne dake jibge a kasuwar: “Wani da bindiga ne ya fara kai ma wani Soja hari a kasuwar, amma sai kwatsam muka samu rahoton fararen hula 12 sun rasa rayukansu.”

Mutane 12 sun gamu da ajalinsu a wani hari da yan ta’addan Mali suka kai wata Kasuwa

Sojojin Mali

Majiyar ya kara da cewa sun gaza samun cikakken bayani game da lamarin, sakamakon wayar tarho bata zuwa yankin da lamarin ya auku, amma yace hukumar Sojin kasa za ta kaddamar da binciken kwakwaf don jin musabbabin harin.

Sai dai wani tsohon ministan kasar kuma dan asalin yankin da aka kai harin ya tabbatar da harin, inda yace shaidun gani da ido sun bayyana cewa harin ya faru ne sakamakon kasassabar Sojojin kasar, ya kara da cewa sama da mutane 15 ne suka mutu.

Kasar Mali ta kwashe shekara da shekaru tana fama da yake yake tsakanin yan ta’adda, kabilun Tuareg da kuma Sojojin kasar, inda a shekarar 2003 kasar Faransa ta aiko da Sojojinta da nufin taimaka ma kasar wajen yakar kungiyar Al-Qaeda da ta shigo kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel