Mutane da dama sun samu rauni yayin da Bom ya tashi a cikin wata Keke Napep

Mutane da dama sun samu rauni yayin da Bom ya tashi a cikin wata Keke Napep

Wani Bom ya tashi a garin Aba na jihar Abia, wanda ya yi sanadiyyar raunata mutane da dama dake gudanar da hada hadarsu a inda ya tashi, kamar yadda gidan rediyon muryar Amurka ta ruwaito.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Asabar 19 ga watan Mayu a kasuwar Yan Doya, inda aka jiyo tashin bama baman a wasu baburan keke Napep, da aka fi sani da suna ‘A daidaita sahu’, wanda hakan ya janyo samun rauni ga mutane da dama.

KU KARANTA: Cakwakiya: wata gada ta rufta da wani Gwamna da mataimakinsa yayin da suke daukar hoton ‘Selfie’

Majiyar Legit.ng ta samu zantawa da wasu daga cikin wadanda suka jikkata, inda suka tabbatar da tashin bam din, kuma suka ce: “Sakamakon tashin Bom dinne wasu karafa suka farfashe, wadanda sune suka raunata mu.”

Mutane da dama sun samu rauni yayin da Bom ya tashi a cikin wata Keke Napep

Garin Aba

Majiyar ta kara da cewa tuni aka garzaya da wadanda abin ya shafa zuwa asibitoci daban daban don samun kulawa, yayinda wasu kuwa sai da ta kai ga an yi musu tiyata domin cire karafan da suka farfasa jikkunansu.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, babu wata kungiya da ta dauki shirya wannan hari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel