Gwaramar Siyasar 2019: Jam’iyyu da yawa da kungiyoyi sun shirya yiwa Buhari taron dangi

Gwaramar Siyasar 2019: Jam’iyyu da yawa da kungiyoyi sun shirya yiwa Buhari taron dangi

- Lokacin zabe na kara kusatowa Jam'iyyu na kara shirin karon batta

- Hadakar Jam'iyyu na kokarin hada hannu don kawar da Buhari a 2019

- Da alama Jam'iyyara APC akwai babban kalubale a gabanta

Wasu kungiyoyi da Jam’iyyun adawa masu burin ganin bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 da suka hada da SDP da LP (Labour Part) da kuma NIM (Nigerian Intervention Movement) sun rattaba hannu wajen hada karfi wuri guda karkashin wani kwamiti domin bin matakan hana Buhari zarcewa.

Gwaramar Siyasar 2019: Jam’iyyu da yawa da kungiyoyi sun shirya yiwa Buhari taron dangi

Gwaramar Siyasar 2019: Jam’iyyu da yawa da kungiyoyi sun shirya yiwa Buhari taron dangi

Shuwagabannin kwamitin sun kunshi manya-manyan jiga-jigai a jam’iyyunsu da kungiyoyinsu

Jaridar Tribune ta rawaito cewa, kundin tsarin mulkin kwamitin an samar da shi ne bayan tuntuba shugabannin jam’iyyun da kungiyoyin a garin Abuja ranar Talata da kuma Juma’a.

An dai rawaito cewa tarurrukan tuntubar an sha gudanar da su a wurare daban-daban kuma sun samu halartar shugabanni daga jam’iyyun Labour Party (LP) da Progressive Party (UPP) da Alliance for New Nigeria (ANN) da Action Democratic Party (ADP) da kuma Action Alliance (AA).

Wakilan SDP sun hada da tsohon Ministan Ilimi Farfesa Tunde Adeniran da kuma sakataren jam’iyyar na kasa Mallam Shehu Gabam tare da Mataimakin shugaban Jam’iyyar Mallam Abdul Ahmed Isiak.

KU KARANTA: Makarfi ya bawa Obasanjo shawara kan yadda za'a hambare gwamnatin Buhari a zaben 2019

Yayinda ayarin Jam’iyyar SDP ya kunshi shugaban Jam’iyyar Y. Y. Sanni da Sakatarensa Dr James Okoroma da Ma’aji.

Kamar yadda ita ma Jam’iyyar NIM ta samu wakilcin shugabanta da sauran Mambobin da suka hada da Dr Abdul Jalil Tafawa Balewa da Dr Elishama Ideh da Daraktan shirye-shirye Hajia Khairat Animashaun.

Wasu daga cikin shugabannin kwamitin da suka bukaci a boye sunansu sun bayyanawa majiyarmu cewa wadannan tarruka yunkuri na kafa babbar rundunar da zata hada karfi da karfe a zaben 2019.

A bisa wannan yarjejeniya da suke shirin kullawa kowanne sashi na hadakar zai sanya hannu a cikin satin nan bayan ya isar da sakon yadda matsayar taron ta kaya ga sauran ragowar Mambobin Jam’iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel