Kyauta kudin Buhari ta farraka kan shugabannin kungiyar Kiristoci ta CAN

Kyauta kudin Buhari ta farraka kan shugabannin kungiyar Kiristoci ta CAN

Kungiyar dattijan Kiristocin kasar nan (NCEF) ta zaqrgi shugabancin kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) da cin da kuma almundahana ta hanyar amfani da mukamin su.

A wata takardar koke da NCEF ta aikewa CAN kuma jaridar Vanguard ta gani, dattijan sun zargi shugabannin CAN da yin mursisi a kan batun kyautar kudin mota da Buhar ya bayar lokacin da CAN karkashin jagorancin shugaban ta, Samson Ayokunle, lokacin da suka kai masa ziyara a watan Nuwambar shekarar da ta wuce.

NCEF ta zargi shugabannin CAN da boye takamaiman adadin kudin da shugaba Buhari ya bayar. A cewar Dattijan, shugaba Buhari ya bawa shugabancin CAN miliyan N40m ne ba N25m ba kamar yadda suka bayyana ba.

Kyauta kudin Buhari ta farraka kan shugabannin kungiyar Kiristoci ta CAN

Buhari dan shugabannin kungiyar Kiristoci ta CAN

Kungiyar dattijan ta bukaci gudanar da bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi a cikin lamarin.

A ranar 10 ga watan Nuwamba ne wakilan kungiyar CAN karkashin jagorancin shugaban ta, Dakta Ayokunle, suka ziyarci shugaba Buhari a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

DUBA WANNAN: Wani tsohon mataimakin gwamna ya fice daga PDP

Kungiyar NCEF na zargin shugabancin CAN da karbar kudi daga hannun shugaba Buhari, mutumin da suka ce ya bari ana kashe kiristoci da gan-gan.

Bayan zargin shugabancin da boye gaskiyar adadin kudin da shugaba Buhari ya bayar, NCEF ta bukaci a binciki shugaban na CAN a kan wasu motoci day a saya a kan farashin da suka ce basu yarda das hi. NCEF ta bukaci a fara tsige Dakta Ayokunle kafin ma a fara bincike a kan sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel