PDP tayi rashi, wani tsohon mataimakin gwamna ya fice daga jam’iyyar

PDP tayi rashi, wani tsohon mataimakin gwamna ya fice daga jam’iyyar

Tsohon mataimakin gwamna a jihar Osun, Sanata Iyiola Omisore, ya bayyana ficewar sa daga jam’iyyar PDP tare da canja sheka zuwa jam’iyyar SDP.

Omisore ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya sakawa hannu da kan sa kuma aka rabawa manema labarai a Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Da yake bayyana irin gwagwarmayar siyasa da ya sha tun daga shekarar 1999, Omisore, ya bayyana cewar, kishin jihar sat a Osun ya saka shi yanke wannan hukunci.

A kwanakin baya ne tsohon gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola, ya bayyana ficewar sa daga jam’iyyar APC tare da marawa sabuwar tafiyar Obasanjo baya.

PDP tayi rashi, wani tsohon mataimakin gwamna ya fice daga jam’iyyar

Iyiola Omisore

A yayin da zabukan 2019 ke kara karatowa, ‘yan siyasa na cigaba da kulle-kulle da kuma canjin sheka domin samun dammar lashe zabe.

DUBA WANNAN: Tura ta kai bango: Jama'a sun dakile wani harin kunar bakin wake da aka kai Masallaci a jihar Yobe

A wani labarin na Legit.ng a yau, kun ji cewar, shugabancin jam’iyyar PDP na fuskantar matsin lamba daga hadakar jam’iyyun Najeriya 36 da kuma tsofin ‘yan jam’iyyar dake cikin APC a kan ta canja sunan ta domin samar da wata jam’iyya da zata fafata da APC a zaben 2019.

Wani bincike da jaridar Punch tta gudanar ya tabbatar da cewar, hadakar jam’iyyu 36 na Najeriya na son PDP ta ajiye sunan tad a alamar ta tare da narkewa cikin wata jam’iyya da ‘yan Najeruya basu kyamar ta. PDP na shirin mika wuya a kan wannan matsin lamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel