An Daure mai Daurewa: ‘Yan sanda 3 sun shiga hannu a dalilin kisan wani saurayi

An Daure mai Daurewa: ‘Yan sanda 3 sun shiga hannu a dalilin kisan wani saurayi

- Rundunar ‘Yan sanda ta bayar da umarnin kame wasu jami’anta guda 3

- ‘Yan sanda dai ana tuhumarsu ne da hannu wajen Mutuwar wani Saurayi mai suna Omonuwa a garin Warri

- Shugaban ‘Yan sanda na shiyya ta 5 ne ya bayar da umarnin kame jami’an bayan Mahaifin Matashin ya shigar da korafi

Mataimakin babban sufeton ‘Yan sanda mai kula da shiyya ta 5 Rasheed Akintunde, ya umarci da a tsare jami’an rundunar su uku wadanda ake zargi da hannu wurin mutuwar wani Matashi mai suna Samson Omonuwa a garin Warri na jihar Delta.

Daurowa take a Daure mai Daurewa: ‘Yan sanda 3 sun shiga hannu a dalilin kisan wani saurayi

Daurowa take a Daure mai Daurewa: ‘Yan sanda 3 sun shiga hannu a dalilin kisan wani saurayi

Mai magana da yawun rundunar ‘Yan sandan na shiyyar DSP Emeka Iheanacho ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) yau 20 ga watan Mayu a Benin.

Kakakin ‘Yan sandan ya ce, "Shugaban shiyyar ya umarci da a damke ‘Yan sandan 3 bayan Mahaifin Saurayin ya shigar da karar mutuwar dansa a ofishin ‘Yan sanda ranar 14 ga watan Mayu."

KU KARANTA: Tura ta kai bango: Yadda jama’a suka dakile harin kunar baki a wani masallaci a Yobe

A don haka ne shugaban ‘Yan sandan na shiyyar ya bukaci iyalan mamacin da sauran jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da bayar da tabbacin cewa rundunar zata yi bincike na hakika domin gano ainihin musabbabin abinda ya faru, kuma duk wanda aka kama da laifi tabbas zai dandani kudarsa.

Daurowa take a Daure mai Daurewa: ‘Yan sanda 3 sun shiga hannu a dalilin kisan wani saurayi

Daurowa take a Daure mai Daurewa: ‘Yan sanda 3 sun shiga hannu a dalilin kisan wani saurayi

Dagan ne ya kuma yi gargadi ga jami’an ‘Yan sandan da su kasance masu bin dokar aiki tare da kare hakkin bil Adama. A cewar Iheanacho

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel