Tura ta kai bango: Yadda jama’a suka dakile harin kunar baki a wani masallaci a Yobe

Tura ta kai bango: Yadda jama’a suka dakile harin kunar baki a wani masallaci a Yobe

Hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewar wasu mutane masu karfin hali sun dakile wani harin kunar bakin wake da wata mata ta kai wani masallaci a garin Gashuwa dake karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

Mataimakin Darektan hulda da jama’a na hukumar soji na rundunar sojin Ofireshon Lafiya Dole, Kanal Onyema Nwachukwu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa day a fitar a Maiduguri, jihar Borno.

Tura ta kai bango: Yadda jama’a suka dakile harin kunar baki a wani masallaci a Yobe

Wata yarinya da aka taba kamawa ta kai harin kunar bakin wake

Wasu al’umma masu karfin halin gaske sun dakile wani mummunan harin kunar bakin wake da wata mata ta kai wani masallaci a garin Gashuwa dake karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

Wata mata daure da bam tayi nasaras shiga cikin Masallaci yayin da jama’a ke kokarin fara sallah amma Allah ya sa wasu mutane suka gan ta yayin da take kokarin tayar da bam din dake jikin ta. Nan da nan suka gaggauta rike ta tare da damka ta hannun dakarun mu dake Azare,” a cewar Kanal Nwachukwu.

DUBA WANNAN: An gano wata tasha a jihar Kano da masu cinikin miyagun kwayoyi ke cin karen su babu babbaka

Kanal Chukwu ya kara da cewa, “jami’an mu na musamman sun kwance jigidar bam din dake jikin matar tare da garzayawa da ita asibiti domin duba raunukan da ta samu yayin da aka kama ta.”

Kungiyar Boko Haram na cigaba da amfani da mata domin kai harin kunar bakin wake a sassan jihar Borno, musamman a Masallatai yayin da jama’a suka taru domin yin Sallah.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel