Rikicin cikin-gidan Jam’iyyar APC ya kara cabewa a Jihohi da dama

Rikicin cikin-gidan Jam’iyyar APC ya kara cabewa a Jihohi da dama

Rigimar da ke cikin Jam’iyyar APC ya ma dai kara kamari bayan an yi zaben shugabannin Kananan Hukumomi da na Jihohi. A da an dai yi tunani cewa zaben zai kawo saukin rikicin cikin gida na Jam’iyyar sai ga akaskin haka.

A irin su Jihar Kogi inda ake rikici tsakanin tsofaffin Shugabannin Jam’iyyar da aka kora da Gwamna Yahaya Bello. Bangaren Hady Ametuo sun yi na su a zaben a wata Makaranta inda bangaren Gwamna su kayi na su a wani filin wasa.

A Jihar Kaduna dai an zabi Air Commodore Emmanuel Jekada daga Zangon-Ketaf a matsayin Shugaban Jam’iyyar mai mulki sai dai ‘Yan taware sun yi na su zaben dabam inda su ka zabi Kanal Gora Dauda Albehu a matsayin Shugaban su.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC na iya samun matsala a zaben 2019

A irin su Kano da Bauchi wadanda ke tare da manyan ‘Yan Majalisar Jihar ba su halarci taron ba. A Jihar Filato ma dai wadanda ba su tare da Gwamnan Jihar sun kauracewa taron inda a Jihar Enugu kuwa aka buge da rigima wajen zaben.

A irin su Jihar Abia, Oyo, Bayelsa da kuma Kwara an samu bangorori inda kowa yake ikirarin shi ne ya fitar da Shugaba. A Legas bangaren Jam’iyyar da ke tare da Jigon Jam’iyyar APC Bola Tinubu sun yi taron su dabam da wasu ‘Yan taware.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel