Idon wasu Malamai ya raina fata sakamakon gicciye wata daliba

Idon wasu Malamai ya raina fata sakamakon gicciye wata daliba

- Horo yayi tsanani ga wasu daliban Makaranta a Yammacin Najeriya

- 'Yan sanda yanzu haka sun damke wadanda ake zargi da zane daliban a gicciye

- Kuma 'Yan sanda na shirin gurfanar da su gaban Kuliya domin hukunci

Kimanin Malamai uku tare da shugaban wata Makaranta a jihar Ogun aka kame sakamakon gicciye wasu dalibai biyu suka zane su a dalilin sun makara zuwa Makaranta kamar yadda jami’an ‘Yan sanda shaidawa tashar Talabijin na CNN.

Idon wasu Malamai ya raina fata sakamakon gicciye wata daliba

Idon wasu Malamai ya raina fata sakamakon gicciye wata daliba

Daliban dai su biyu an gicciye su ne a gaban Makarantar ta su ana zane su a safiyan ranar Laraba a kauyan Ayetoro na jihar Ogun.

KU KARANTA: 2019: Cikin sati uku zamu narke cikin wata jam’iyyar – Jigo a jam’iyyar PDP

Kakakin rundunar ‘Yan sanda na jihar ta Ogun Abimbola Oyeyemi ya shaidawa CNN cewa, a "An daure yaran ne a jikin katako ana zane su ne sai ‘Yan sandan dake sintiri suka yi arba da su, sannan suka umarci mai Makarantar da su kunce daliban amma suka ki. Hara ta kai ga sun daki wani Mutumi da ya sanya baki kan maganar."

Yanzu haka dai rundunar ‘Yan sanda ta jihar tayi bincike kan lamarin kuma ana cajin shugaban Makarantar da sauran Malaman da laifin cin zarafi da kuma mugunta da kaiya yin illa. Kamar yadda jaridar Eagle ta rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel