N-PDP: Shugaba Buhari ya ki ganawa da su Kwankwaso da Wammako

N-PDP: Shugaba Buhari ya ki ganawa da su Kwankwaso da Wammako

Tun kwanaki ne wasu tsofaffin ‘Yan Jam’iyyar PDP da ke cikin APC a yanzu su ka aikawa Shugaban kasa Buhari takarda inda su ka koka da ware su da aka yi a Gwamnati. Nuhu Baraje da Olagunsoye Oyinlola su ka sa hannu kan wasikar.

‘Yan N-PDP irin su Tsofaffin Gwamna Rabiu Kwankwaso da Aliyu Wammako wanda su ke Majalisar Dattawa a yanzu da kuma tsohon Kakakin Majalisa Aminu Tambuwal da su ka taka rawar gani a 2015 sun ce an maida su saniyar ware a APC.

N-PDP: Shugaba Buhari ya ki ganawa da su Kwankwaso da Wammako

Shugaba Buhari yayi banza da batun ‘Yan n-PDP

Tuni dai har wa’adin da manyan ‘Yan siyasar su ka ba Shugaban kasar ya wuce kuma ba a dauki wani mataki ba. Sauran wadanda ke cikin irin wannan tafiyar irin su Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da kuma Rt. Hon. Yakubu Dogara.

Da tsofaffin ‘Yan siyasar ne dai aka yi amfani aka karbe mulki daga PDP sai dai kuma yanzu kusan Tsohon Gwamnan Ribas Rotimi Amaechi ne kurum aka tafi da shi a Gwamnatin Buhari don haka su ke nuna cewa idan aka yi sake abubuwa za su canza.

KU KARANTA:

Sai dai kusan duk manyan ‘Yan siyasar irin su Kwankwaso sun samu matsala da Gwamnan Kano na yanzu watau Abdullahi Ganduje kuma Gwamnonin za su yi amfani da karfin kujerar su wajen nakasa irin su Kwankwaso kuma su ga Buhari ya ci 2019.

Kwanaki dai Shugaba Buhari ya kara nuna farin jinin sa a Jihar Jigawa da ya kai ziyara. Sai dai duk da haka Jam’iyyar ta APC na iya samun matsala idan wadannan manyan ‘Yan siyasa su ka janye hannun su daga Jam’iyyar ko su ka sauya sheka gaba daya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel