Likafa ta cigaba: Magu ya samu wani babban mukami a nahiyar Afrika

Likafa ta cigaba: Magu ya samu wani babban mukami a nahiyar Afrika

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) na rikon kwarya, Ibrahim Magu, ya zama shugaban gamayyar hukumomin yaki da cin hanci na kasashen kungiyar Commonwealth dake nahiyar Afrika.

Shugabannin hukumomin sun amince da zaben Magu a matsayin shugaba a karshen wani taro na kwanaki biyar da suka kamma a birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Taron na shugabannin hukumomin yaki da cin hanci ya tattauana a kan yadda za a shawo kan matsalolin wawure dukiyar kasashen Afrika da wasu shugabanni ke yi tare da jibge su a kasashen ketare tare da tattauna hanyoyin da za a bi domin kwato wadanda aka karkatar a ciki da wajen nahiyar Afrika.

Likafa ta cigaba: Magu ya samu wani babban mukami a nahiyar Afrika

Ibrahim Magu

Kazalika taron ya shawarci gwamnatocin Afrika das u bawa tsarin tona asirin masu cin hanci fifiko a matsayin wata hanya da zata iya kawo saurin gano masu cin hanci da rashawa.

DUBA WANNAN: PDP tayi bakin jini, zamu canja sunan jam'iyyar - Jigo a jam'iyyar PDP

Gwamnatin shugaba Buhari c eta fara kirkiro dokokin fallasa kudaden sata, lamarin day a kai ga gwamnatin ta bankado kudade masu dumbin yawan gaske da wasu jami’an gwamnati suka sata kuma suka boye su a wasu wurare a cikin kasar.

A satin day a gabata ne shugaba Buhari ya kaddamar da sabon ginin shelkwatar hukumar EFCC day a lashewa gwamnatin kasar biliyan N24bn.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel