Wani rikakken Malami a Kasar Japan yayi nazari kan fa’idar barin ciki da yunwa

Wani rikakken Malami a Kasar Japan yayi nazari kan fa’idar barin ciki da yunwa

A daf da karshen shekarar 2016 wani Malami a wata Jami’a a Kasar Japan Yoshinori Ohsumi ya samu lambar kyauta ta Nobel ta Duniya a dalilin wani nazari da yayi kan fa’idar azumi.

Wannan Malamin da ke Birnin Tokyo yayi bincike ne kan wani abu da ake kira “Autophagy”. Wannan dai ba wani abu bane illa yadda jikin mutum ke canza wasu bangare na kwayoyin rai da su ke mutuwa a jikin mutum ya zama ba su da amfani.

Kamar dai yadda ake canza batir ko taya ko wasu bangaren tsohuwar mota, haka ake sauya wasu sashe na kwayoyin rai a jikin Bil Adama idan amfanin su ya kare. Idan an canza su da wasu sababbi sai kwayoyin su kara lafiya a jikin mutum.

KU KARANTA: Goron Ramadan: Abubuwa 5 da ke karya azumin Musulmi

Hanya mafi sauki da ake canza wadannan rubabbun bangarori shi ne ta hana jiki abinci. Azumi na cikin wannan hanya kuma yana taimakawa Musulmai a jikin su. Dadewa ba tare da abinci ba zai sa wadannan bangarori su mutu a samu wasu.

Yunwa tana sa sinadarin glucagon yayi sama yayin da shi kuma insulin zai yi kasa. Da zarar glucagon yayi kasa dai wasu bangarorin jikin mutum su ke kwararrabewa domin a samu gurbin kafa sababbin sashe inji manyan kwararrun Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel