‘Yan taware sun bayyana a bangaren Jam’iyyar APC na Legas

‘Yan taware sun bayyana a bangaren Jam’iyyar APC na Legas

Rigimar da ke Jam’iyyar APC ta kai Jihar Legas inda mu ke jin cewa an yi zabuka daban-daban a makon nan. Wasu dai sun yi taron su a ofishin Jam’iyyar ne yayin da wasu da su ka ware daga uwar Jam’iyya su kayi nasu taron a wani otel.

Ainhin bangaren Jam’iyyar wanda kuma su ke tare da Jigon Jam’iyyar na kasa Bola Tinubu sun yi taron su a Sakatariyar Jam’iyya inda aka zabi Tunde Balogun a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Legas a karshen makon nan.

‘Yan taware sun bayyana a bangaren Jam’iyyar APC na Legas

Wasu 'Yan APC sun yi baram-baram da umarnin Tinubu

Sai dai wasu da su ka ware a gefe guda sun yi na su taron ne a otel din Ikeja Airport inda su ka zabi Fuad Okaji a matsayin Shugaban su. Sanni Oloye da kuma Wole Oshodi ne su ka zama Mataimakin sa da kuma Sakataren sa.

KU KARANTA: Ana ta takaddama tsakanin 'Yan Sanda da Saraki

Fuad Okaji ne Shugaban yakin neman zaben Bola Tinubu da Raji Fashola da Akinwumi Ambode a lokacin su na neman Gwamna. Shi kuma dai Tunde Balogun da Jam’iyya ta zaba tsohon Kwamishi na ne na Jihar Legas a da.

Sakataren yada labarai na Jam’iyyar Joe Igbokwe da kuma ‘Dan Majalisar Jihar Abiodun Faleke sun ce bangaren Oki sun bata lokacin su ne kurum a banza. A Legas dai an samu ‘Yan taware a Jam’iyyar kamar wasu Jihohin na APC.

Cif Sunny Ajose Funsho Ologunde, Kayode Olusanya, Hakeem Bamigbala, Ahmed Joana Adebobuyi, Joe Igbokwe, Abiodun Salami, Ademola Sadiq su na cikin sauran da aka zaba a matsayin Shugabannin Jam’iyyar a Legas.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel