Hazikar ‘Daliba ta karbi kyatuttuka rututu a Makarantar Atiku Abubakar

Hazikar ‘Daliba ta karbi kyatuttuka rututu a Makarantar Atiku Abubakar

- Jami’ar AUN da ke Yola ta yaye ‘Daliban ta na wannan shekarar

- Fatimah Jauro daga Arewacin Najeriya ta taka rawar gani a bana

- Hazikar ‘Dalibar ta ciri tuta a bangaren ilmin tattalin arzikin Kasa

Mun samu labari cewa wata ‘Daliba ‘Yar Baiwa ta kafa tarihi a Jami’ar American Univeristy da ke Najeriya watau AUN inda ta tashi da kyatuttuka iri-iri a wajen bikin yaye ‘Daliban Makarantar. Sunan wannan 'Daliba Fatima Abubakar Jauro.

Hazikar ‘Daliba ta karbi kyatuttuka rututu a Makarantar Atiku Abubakar

Fatima Jauro ta karbi kyautar hazaka a bana Hoto daga: Mu'awiya Muye/Twitter

Fatimah Jauro ce ta ci lambar yabo a matsayin ‘Dalibar da ta fi kowa bada himma a bangaren tattalin arziki. A makon nan ne Jami’ar ta yaye ‘Daliban ta na shekarar 2018 inda Benedict Egwuchukwu ya zama wanda yayi zarra a Jami’ar.

KU KARANTA: Abin da ya fi komai wahala a wajen mulki - Buhari

Hazikar ‘Daliba ta karbi kyatuttuka rututu a Makarantar Atiku Abubakar

Wani daga cikin lambar yabon da aka ba Fatima Jauro

A bangaren wadanda su ka karanta ilmin tattalin arziki dai wannan Baiwar Allah da ta fito daga Arewacin Kasar ce a gaba. Bayan nan kuma Fatimah Jauro ce ta ciri tuta a gaba daya tsangayar ilmin Jama’a da da mu’umular su a kaf Jami’ar.

Fatimah Jauro ta fi kowa adadin maki na CGPA a tsangayar ta. Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya jinjinawa ‘Daliban Makarantar a wajen taron yaye ‘Daliban na bana wanda shi ne karo na 10 a tarihin katafariyar Jami’ar.

Hazikar ‘Daliba ta karbi kyatuttuka rututu a Makarantar Atiku Abubakar

Fatima Abubakar Jauro ta ba mazan AUN kunya

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel