Tarihi ya maimata kan sa bayan shigen abin da su ka wakana shekaru 37 sun kuma faruwa

Tarihi ya maimata kan sa bayan shigen abin da su ka wakana shekaru 37 sun kuma faruwa

Masana ilmin tarihi sun bayyana mana cewa tarihin ya maimata kan sa wannan shekarar bayan shigen abin da ya faru kusan shekaru 40 da su ka wuce ya sake aukuwa a bana. Daga cikin manyan abubuwan da su ka faru a shekarar 1981 su ka sake faruwa bana akwai:

Tarihi ya maimata kan sa bayan shigen abin da su ka wakana shekaru 37 sun kuma faruwa

A bana ma za a kara tsakanin Real Madrid ta Liverpool

1. Mahathir Mohammed ya zama Shugaban kasa

Mahathir Mohammed ya mulki Kasar Malaysia na fiye da shekaru 22 kafin ya sauka daga mulki a 2003. A shekarar ta 1981 ne Mahathir Mohammed ya zama Shugaban kasa kuma yanzu a 2018 ya sake dawowa kujerar yana ‘Dan shekara sama da 90.

KU KARANTA: Shugaban Najeriya a sabon ofishin Hukumar EFCC

Tarihi ya maimata kan sa bayan shigen abin da su ka wakana shekaru 37 sun kuma faruwa

A shekarar 1981 Yarima Charles ya auri Lady Diana

2. Daurin auren gidan sarautar Ingila

A tsakiyar shekarar 1981 ne aka yi auren Yarima Charles na Kasar Wales ta Birtaniya da kuma Lady Diana Spencer. Amaryar dai ba ‘yar gidan manya bace a lokacin. A bana ma dai Yarima Henry na gidan Sarautar ya auri Meghan Markle.

3. Wasan Zakarun Turai tsakanin Madrid da Liverpool

A irin wannan lokacin a shekarar 1981 dai Liverpool ta doke Kungiyar Real Madrid a wasan karshe na cin-kofin Zakarun Nahiyar Turai da ci 1-0. A bana ma dai kuma an sake haduwa tsakanin manyan Kungiyoyin kwallon kafan na Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel