An nada sabbin Dagatai 77 a jihar Kaduna

An nada sabbin Dagatai 77 a jihar Kaduna

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, gwamnatin jihar Kaduna ta nada sabbin dagatai na gundumomi 77 sakamakon sabon sauye-sauye na tsara yankuna a jihar.

Babban hadimin gwamnan jihar akan hulda da manema labarai, Samuel Aruwan, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Asabar din da ta gabata.

Mista Samuel ya bayyana cewa, wannan sabbin nade-nade ya zo ne a sakamakon kammala sauye-sauye na tsara yankuna a jihar.

An nada sabbin Dagatai 77 a jihar Kaduna

An nada sabbin Dagatai 77 a jihar Kaduna
Source: Depositphotos

A sanadiyar haka ne masarautar jihar ta bayar da sunaye 230 na masu neman kujerun dagaci a jihar, inda bayan an kammala tantancewa gwamnatin jihar ta fitar da 77 daga cikin su.

Yake cewa, wannan sabbin nade-nade sun dawo da tsari na adadin gundumomi da suka kasance tun gabannin shekarar 2001.

KARANTA KUMA: Ababe 4 da ya kamata ku sani game da Sabuwar Amaryar Masarautar Ingila

Aruwan ya kara da cewa, wannan lamari yana daya daga cikin manufofi na gwamnatin Mallam Nasir El-Rufa'i dangane da rage adadin gundumomi da ya kudirta tun a watan Yunin 2017 kamar yadda jihar ta kasance shekaru 17 da suka gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin jihar ta yanke wannan shawara ne bayan tuntube da kusoshi na masarauta dake cikin kauyuka da gundumomi a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel