Uche Secondus da Wasu Jiga-Jigan Jam'iyya na fuskantar Barazana ta APC - PDP

Uche Secondus da Wasu Jiga-Jigan Jam'iyya na fuskantar Barazana ta APC - PDP

A ranar Asabar din da ta gabata ne jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa, shugaban ta Cif Uche Secondus da wasu jaga-jigan jam'iyyar na fuskantar babban kalubale mai cike da barazana.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, kakakin jam'iyyar Mista Kola Ologbondiyan, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a babban birnin kasar nan na tarayya.

Mista Kola ya bayyana cewa, jam'iyyar APC ta daura damarar sanya takunkunmi kan wasu jiga-jigan jam'iyyar ta PDP a sakamakon yunkurin su na tsayawa takara da za su fafata da shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen neman kujerarar sa a zaben 2019.

Uche Secondus da Wasu Jiga-Jigan Jam'iyya na fama da Barazana - PDP

Uche Secondus da Wasu Jiga-Jigan Jam'iyya na fama da Barazana - PDP
Source: Depositphotos

Kakakin ya ci gaba da cewa, wannan barazana tana cin karo da tanadi na dimokuradiyyar kasar nan, inda ya nemi kasashen ketare akan su sanya idanun su cikin lamarin kasar nan.

KARANTA KUMA: Likitoci sun raba wasu Tagwaye da aka haifa manne da juna a birnin Yola

Ya kara da cewa, jiga-jigan jam'iyyar su musamman shugaaban ta na kasa, ya fara fuskantar barazana tun yayin da jam'iyyar ta shigar da korafi zuwa ga kungiyar hadin kan kasashe ta duniya dangane da yadda jam'iyyar APC ke kalubalantar dimokuradiyyar kasar nan.

Legit.ng ta fahimci cewa, korafin jam'iyyar ta PDP ya hadar har da yadda gwamnatin tarayya ke mulkin kama karya, keta haddin dan Adam, kashs-kashe, yiwa shari'a karan tsaye da sauran muzguni dake cin karo da tanadi na kundin tsarin mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel