Ainihin dalilin da yasa aka dawo da yan bindigan da ake alankatawa da Saraki Abuja

Ainihin dalilin da yasa aka dawo da yan bindigan da ake alankatawa da Saraki Abuja

Siyasa da sanin manyan mutane ka iya zama babban dalilin da yasa aka dawo da yan bindigan da ake alakantawa da Saraki Abuja daga ofishin hukumar yan sandan da ke Ilori, jihar Kwara.

Amma hukumar yan sanda ta bayyana cewa ta dau wannan mataki ne domin zurfafa bincike cikin wannan al’amari.

Wasu makasa 6 sun shiga hannun hukumar yan sandan Najeriya wadanda suk kasance suna halaka rayukan jama’a a shekarun baya a jihar Kwara.

Shugaban majalisar dattawa ya kai kuka kujeran shugaba Buhari cewa babban sifeton hukumar yan sanda, IGP Ibrahim Idris, na kokarin alakantashi da wasu makasa da hukumar ta damke.

Ainihin dalilin da yasa aka dawo da yan bindigan da ake alankatawa da Saraki Abuja

Ainihin dalilin da yasa aka dawo da yan bindigan da ake alankatawa da Saraki Abuja

Amma wata majiyar hukumar ta bayyana jiya cewa babban dalilin da zai sa a dauke yan baranda daga wani jiha zuwa Abuja shine idan ana tsoron wasu zasu iya kawo cikas.

Majiyar tace: “Duk da cewa duk wanda aka kama na da hakkin kula kamar mai gaskiya har sai an kamashida laifi karara, wasu daga cikinsu na da madogara masu karfi ciki da wajen hukumar.”

Majiyar ta kara da cewa da daya daga cikin makasan ‘da ne ga wani babban mai rawani a masarautar Ilori kuma tsohon kakakin hukumar yan sanda a jihar.

KU KARANTA: Tsoffin Gwamnoni da Mataimakansu 21 da suke karbar Albashi har sau biyu

“Bugu da kari, babban yayanshi shine shugaban hukumar yan sandan SARS a wani jihan Yarbawa.”

“A yanzu haka, an canza wajen aikin mataimakin kwamishanan yan sandan jihar Kwara saboda wasu dalilai da bai bayyana ga jama’a ba illa shugabanni a Abuja.”

Kakakin hukumar yan sanda, ACP Moshood Jimoh, ya ki Magana da yan jarida game da wannan abu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel