Ya zuwa yanzu: Barkewar Ebole ta zama babbar annoba a Congo - WHO

Ya zuwa yanzu: Barkewar Ebole ta zama babbar annoba a Congo - WHO

- Ballewar cutar Ebola na barazana ga kasar Congo ta tsakiyar Afirka

- Ana tsoron tsallakawar cutar kasashe masu makwabtaka

- Ebola tana da saurin yaduwa daga taba juna

Ya zuwa yanzu: Barkewar Ebole ta zama babbar annoba a Congo - WHO

Ya zuwa yanzu: Barkewar Ebole ta zama babbar annoba a Congo - WHO

Hukumar lafiya ta duniya ta sake karin haske kan yiwuwar cutar Ebola da ta barke a kasar Congo mai yawan dazuka, fadin kasa da jama'a inda tace watakil cutar ya zuwa yanzu ta kama hanyar fin karfin ikon jami'anta.

Idan cutar ta bazu kamar wutar daji tana iya shafar kasashe makwabta, musamman gabashiin Najeriya inda yawancin mutanen Kamaru kan tsallako domin saye da sayarwa. Ya zuwa yanzu dai mutane 45.

DUBA WANNAN: Najeriya na kokari kan lantarki ta Nukiliya

An sami shigar cutar ne wani birni dake kasar mai suna Mbandaka wanda ke da jama'a daga kasashen waje da suke zuwa kasuwanci.

An aika magungunan riga-kafi ga kasar an kuma killace wadanda cutar ta kama, amma lamarin na iya bijirewa kokarin hukumar ta duniya. Dama dai Ebola tana fin karfin kasashen da ta kama musamman gwamnatocin kasashen da basu da kwari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel