Sabuwar doka: Ku fara cacike jami'in dan sandan da duk yace zai cacike ku

Sabuwar doka: Ku fara cacike jami'in dan sandan da duk yace zai cacike ku

Hukumar rundunar 'yan sanda a Najeriya ta shaidawa 'yan Najeriya wanzuwar wata dokar da ke zaman sabuwa a gare su da ta basu damar su fara cacike dukkan jami'in dan sandan da ya bukaci ya cacike su yayin da yake wani bincike.

Hukumar ta 'yan sandan dai ta shelanta hakan ne a shafin su na dandalin sadarwar zamani na Tuwita mai adreshin @PoliceNG a ranar Alhamis din da ta gabata a kokarin da take yi na wayar wa da al'umma kai.

Sabuwar doka: Ku fara cacike jami'in dan sandan da duk yace zai cacike ku

Sabuwar doka: Ku fara cacike jami'in dan sandan da duk yace zai cacike ku

Legit.ng ta samu cewa sai dai wannan tanadin na doka ya jawo tafka muhawara sosai a tsakanin 'yan Najeriya inda wasu ke ganin yin hakan tamkar tarar aradu ne da ka musamman ma ganin yadda jami'an a cewar su ba su da kirki ko kadan.

A wani labarin kuma, Dalibai biyu daga jami'ar tarayyar ta fasaha da ke garin Akure babban birnin jihar Ondo watau Federal University of Technology, Akure (FUTA), masu sunayen Taofeek Olalekan Afeez da kuma Alayande Abdulwaheed Abiola sun kirkiro wata na'ura mai ban al'ajabi.

Kamar dai yadda muka samu, na'urar da suka kirkiro ta samu nasarar lashe masu gasar kirkire-kirkire da kamfanin nan na fasahar zamani na Microsoft ya saka a Najeriya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel