Rikicin Jam'iyya: Dogara da wasu Mutane 9 sun yi korafin Oyegun har Gaban Kuliya

Rikicin Jam'iyya: Dogara da wasu Mutane 9 sun yi korafin Oyegun har Gaban Kuliya

Wani sabon rahoto da sanadin shafin jaridar The Nation ya bayyana cewa, Kakakin Majaliasar Wakilai, Hon. Yakubu Dogara da wasu mutane tara sun yi karar shugaban jam'iyyar APC, Cif John Odigie-Oyegun har gaban babbar kotun tarayya dake garin Abuja.

Jaridar dai ta ruwaito cewa, wannan mutane sun yi korafin shugaban jam'iyyar ne dangane da taron mazabu da kananan hukumomi na jam'iyyar a jihar Bauchi.

Masu korafin dai sun yi ikirarin cewa, yanayi na gudanar da tarukan ya ci karo da dokoki da sharudda dake cikin tanadi na kundin tsari da jam'iyyar ta gindaya.

Rikicin Jam'iyya: Dogara da wasu Mutane 9 sun yi korafin Oyegun har Gaban Kuliya

Rikicin Jam'iyya: Dogara da wasu Mutane 9 sun yi korafin Oyegun har Gaban Kuliya

Rahotanni sun bayyana cewa, masu korafin sun nemi kotun da ta dakatar da taron jam'iyyar da aka shirya gudanarwa a ranar yaubta Asabar a jihar su sakamakon korafin da riga da gabata a gaban kotun.

KU KARANTA: Rigar Kowa: Anyi Jana'izar Surukin Obasanjo a jihar Edo

Hasashen manema labarai ya bayyana cewa, ta yiwu wannan shine yaki na karshe da Dogara zai fafata karkashin lema ta jam'iyyar APC kafin ya sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Legit.ng ta fahimci cewa, wadansa ake korafin sun hadar da shugaban jam'iyyar Oyegun, sakataren jam'iyyar na kasa, shugaban jam'iyyar na jihar; Dakta Tony Macfoy da Mista Sam Para.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel