Dalibai 2 daga jami'ar Najeriya sun kirkiro wata na'ura mai ban al'ajabi

Dalibai 2 daga jami'ar Najeriya sun kirkiro wata na'ura mai ban al'ajabi

Dalibai biyu daga jami'ar tarayyar ta fasaha da ke garin Akure babban birnin jihar Ondo watau Federal University of Technology, Akure (FUTA), masu sunayen Taofeek Olalekan Afeez da kuma Alayande Abdulwaheed Abiola sun kirkiro wata na'ura mai ban al'ajabi.

Kamar dai yadda muka samu, na'urar da suka kirkiro ta samu nasarar lashe masu gasar kirkire-kirkire da kamfanin nan na fasahar zamani na Microsoft ya saka a Najeriya.

Dalibai 2 daga jami'ar Najeriya sun kirkiro wata na'ura mai ban al'ajabi

Dalibai 2 daga jami'ar Najeriya sun kirkiro wata na'ura mai ban al'ajabi

KU KARANTA: Yan sanda sun kama Yahudawa 70 a Najeriya

Legit.ng ta samu cewa daliban biyu da ke karatun digirin su na farko a fannin ingjiniya sun kirkiro na'urar da za ta iya rage hatsarin kamuwa da cutar daskarewar jini a jikin dan adam.

Yanzu dai daliban za su wakilci Najeriya ne inda za su sake karawa da wasu mutanen daga kasashe akalla 28 a dukkan fadin duniya domin gwabzawa da nufin lashe kayautar makudan kudaden da suka kai dala dubu dari.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel