Naira ta sha kasa a kasuwannin canji na bayan fage, karanta sabon farashin ta

Naira ta sha kasa a kasuwannin canji na bayan fage, karanta sabon farashin ta

Darajar kudaden Najeriya na Naira ta sha kasa a kasuwannin canji na bayan fage a jahohin Najeriya da dama kamar dai yadda kamfanin dillacin labarai na Najeriya ya shaida mana.

A cewar majiyar ta mu, Naira din ta rasa darajar ta ne da akalla digo tara wanda hakan kuma ya jaza aka rika fansar dalar Amurka a kan Naira 363 a maimakon Naira 362 a satin da ya gabata.

Naira ta sha kasa a kasuwannin canji na bayan fage, karanta sabon farashin ta

Naira ta sha kasa a kasuwannin canji na bayan fage, karanta sabon farashin ta

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun yi wa 'yan Boko Haram luguden wuta

Legit.ng ta samu cewa haka zalika a kasuwar 'yan canjin Naira 502 ne ake canzar kudin Ingila na Pound sannan kuma Naira 428 ake canzar kudin tarayyar Turai na Euro.

A wani labarin kuma, Dalibai biyu daga jami'ar tarayyar ta fasaha da ke garin Akure babban birnin jihar Ondo watau Federal University of Technology, Akure (FUTA), masu sunayen Taofeek Olalekan Afeez da kuma Alayande Abdulwaheed Abiola sun kirkiro wata na'ura mai ban al'ajabi.

Kamar dai yadda muka samu, na'urar da suka kirkiro ta samu nasarar lashe masu gasar kirkire-kirkire da kamfanin nan na fasahar zamani na Microsoft ya saka a Najeriya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel