Yanzu-Yanzu: Sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a sansanin 'yan Boko Haram

Yanzu-Yanzu: Sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a sansanin 'yan Boko Haram

Jami'an rundunar sojojin saman Najeriya watau Nigerian Air Force (NAF) a takaice a jiya sun sanar da samun nasarar yin luguden wuta akan sansanonin 'yan ta'addan Boko Haram a kauyukan da ke garuruwan Bama, jihar Borno.

Kamar dai yadda sanarwar da rundunar ta fitar, sun ce jami'an leken asirin su ne suka gano maboyar ta 'yan Boko Haram din kafin daga bisani suyi masu luguden wuta.

Yanzu-Yanzu: Sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a sansanin 'yan Boko Haram

Yanzu-Yanzu: Sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a sansanin 'yan Boko Haram

KU KARANTA: Zuwan Buhari tafsir ya bar baya da kura

Legit.ng ta samu haka zalika cewa, jami'in hulda da jama'a na rundunar Air Vice OlatokunboAdesanya ya bayyana cewa rundunar za ta cigaba da yin iya bakin kokarin ta domin ganin ta kakkabe dukkan sauran birbishin 'yan ta'addan.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa jami'an tsaron Najeriya sun yi nasarar cika hannuwan su da wasu 'yan Najeriya da suke ikirarin cewa suna bin addinin yahudawa a gidan hatsabibin nan Nnamdi Kanu.

Makwaftan gidan na Nnamdi Kanu da yanzu haka ba'a san inda yake ba dai sun ce ranakun Juma'a da Asabar din satin da ya gabata sun rasa samun sukunin yin harkokin su sakamakon ayyukan ibadar da yahudawan ke yi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel