Hukumar EFCC ta taso keyar wani na hannun daman Bukola Saraki

Hukumar EFCC ta taso keyar wani na hannun daman Bukola Saraki

- Hukumar EFCC tana gudanar da bincike a kan Bamikole Omishore, hadimin shugaban majalisa Bukola Saraki

- Ana zarginsa ne da ware wa matarsa albashin na N150,000 duk wata duk da cewa ita ba ma'aikaciyar majalisar bane

- Mr Omishore ya musanta aikata wani laifi amma baiyi tsokaci a kan zargin da akayi na cewa yana amfani da sunan matasara yana karaban albashi ba

Jami'an hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'anti (EFCC) suna gudanar da bincike kan wani hadidimin Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki mai suna Bamikole Omishore wanda ake zargi da ware wa matarsa albashi duk da cewa ita ba ma'aikaciya bane.

EFCC ta tiso keyar wani na hannun daman Bukola Saraki

EFCC ta tiso keyar wani na hannun daman Bukola Saraki

Wata majiya daga hukuma EFCC ta sanar da jaridar Premium Times cewa hukumar ta fara gudanar da bincike a kan Mr Omishore kuma akwai yiwuwar za'a kama shi nan da kankanin lokaci.

KU KARANTA: Dubi yadda zaka iya caje 'dan sanda bayan ya tsare ka a hanya ko yazo maka gida - Hukumar 'Yan sanda

A yammacin jiya Juma'a mai magana da yawun hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya ce "A halin yanzu muna gudunar da bincike a kan lamarin."

Mr Omishore ya musanta cewa ya aikata wani laifi da sunansa ko kuma a madadin uwargidansa a yayinda Premium Times ta tuntunbe shi a jiya Juma'a sai dai baiyi tsokaci a kan zargin da akeyi na cewa uwargidansa na karbar albashi daga majalisar tarayyar ba duk da cewa bata aiki a majalisar.

A watan da ta gabata ne wata kungiyar masu yaki da rashawa suka shigar da kara ga hukumar ta EFCC inda suka bayyana yadda Mr Omishore mai shekaru 35 ya sanya sunan uwargidansa a cikin ma'aikantan majalisar kuma ta rika karban albashi.

A takardan koken da kungiyar ta shigar wa EFCC wanda jaridar Punch ta wallafa ya bayyana cewa Abiola Omishore tana zama ne a kasar Amurka inda ta ke aiki a matsayin ma'aikaciyar jinya na asibiti amma tana karbar albashin N150,000 duk wata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel