Jirgin sama dauke da fasinjoji 104 ya yi hatsari a kasar Cuba

Jirgin sama dauke da fasinjoji 104 ya yi hatsari a kasar Cuba

- Wata hatsarin jirgin sama mai muni da faru a kasar Cuba

- A kalla fasinjoji 100 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin

- Ma'aikatan lafiya sun garzaya wurin da hatsarin ya faru don taimakawa wadanda suka raunana

A kalla mutane 100 ne suka rasu bayan wani jirgin sama kirar Boeing 737 ya fado kusa da filin jirgin sama na Jose Marti International da ke garin Havana babban birnin kasar Cuba.

Mutane uku sun tsira da rayukansu amma suna samu raunuka masu tsanani kamar yadda jaridar Granma ta ruwaito.

Jirgin sama dauke da fasinjoji 104 ya yi hatsari a kasar Cuba

Jirgin sama dauke da fasinjoji 104 ya yi hatsari a kasar Cuba

DUBA WANNAN: Dubi yadda zaka iya caje 'dan sanda bayan ya tsare ka a hanya ko yazo maka gida - Hukumar 'Yan sanda

Jirgin dai yana hanyarsa ne na zuwa garin Holuguin yayinda hatsarin ya faru.

Jirgin ya fadi ne a tsakanin Boyeros da kuma kauyen Santiago de La ve yigas da ke tazarar kilo mita 20 kudu da birnin Havana kamar yadda gidan talabijin na kasar ya ruwaito.

Jirgin yana dauke da fasinjoji 104 ne da kuma mai'aikatn jirgin guda tara

Shugaban kasar ta Cuba Miguel Diaz-Canel ya ziyarci inda jirgon saman ya fadi kuma ya bayyana hatsarin a matsayin abin jimami: "Wannan hatsarin abin tayar da hankali ne. Bisa dukkan alamu mutane kalilan ne suka tsira da rayukansu."

Tuni ma'aikatan bayar da taimakon gagagwa da motocin daukar marasa lafiya sun hallarci inda jirgin ya fadi don kashe gobara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel